✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu kai wa ’yan sanda hari su kuka da kansu —Buhari

Buhari ya lashi takobin sa kafar wando da masu kai hari cibiyoyin ’yan sanda.

Shugaba Muhammadu Buhari ya lashi takobin sanya kafar wando da masu kai wa cibiyoyin ’yan sanda hari ko neman tayar fitina a Najeriya.

Ya kuma nanata cewa umarninsa na bindige duk wanda aka yi arba da shi dauke da bindiga ba bisa ka’ida ba tana nan tana aiki.

“Duk kasar da mayar da jami’an ’yan sandanta da cibiyoyinsu abin kai wa hari, to na gab da durkushewa; Za mu dauki tsattsauran mataki kan ko waye ya kai wa ’yan sanda ko wasu jami’an tsaro hari,” a cewar Buhari.

A baya-bayan nan, haramtacciyar kungiyar IPOB mai neman ballewa daga Najeriya ta kafa kasar Biafra, ta tsananta kai wa cibiyoyin ’yan sanda da wasu gine-ginen gwamnati hare-hare a yankin Kudu maso Gabas.

“Na umarci Shugaban ’yan sanda ya tashi ya dawo musu da karsashinsu, musamman lura da tarzomar zanga-zangar #EndSARS da hare-haren da ake kai wa cibiyoyin ’yan sanda a baya-bayan nan.

“Zan maimaita, umarnin da na ba wa jami’an tsaro na su harbe duk wanda aka samu da bindiga kirar AK-47 ko sauran muggan makamai na nan tana kan aiki.

“A matsayina na Babban Kwamandan Tsaron Kasa, aikina na farko shi ne tsaron kasa da kuma kare rayuka da lafiyar mutanen cikinta.

“Duk da dimbin kalubale da muke fuskanta, ’yan Najeriya su kawan da sanin cewa za mu samar musu da tabbataccen tsaron rayuka da dukiyoyi a yankunansu da manyan hanyoyi da kuma dazuka,” inji shi.