’Yan bindiga sun sako masu ibada 60 suka sace a Cocin Emmanuel Baptist da ke Jihar Kaduna sun kubuta.
Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), Reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab, ya ce an sako masu idabar ne a ranar Juma’a tare da wasu mutum tara da su ma aka yi garkuwa da su.
- An kama ‘likita’ ya yi wa hannunsa basaja don guje wa rigakafin COVID-19
- Gambiya: Me zai biyo bayan zaben shugaban kasa?
“Tabbas an sako ’yan cocin Kakau jiya (Juma’a) da dare kuma cocin ya shaida min cewa ya taka muhimmiyar rawa, don haka ina yaba musu,” inji shi.
Rabaran Hayab bai bayyana ko an biya kudin fansa ba, amma ya ce bayan an sako mutanen sojoji sun wuce da su zuwa bariki.
Masu garkuwar sun sako mutanen ne bayan wata guda da suka sace su a cocin da ke yankin Kakau Daji a Jihar Kaduna.
A ranar 31 ga Oktoba ne maharan suka yi wa cocin dirar mikiya suka tisa keyar mutum akalla 60.