Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce duk masu hannu a kisan fitaccen dan siyasa, Ahmed Gulak a garin Owerri na Jihar Imo za su fuskanci tsattsauran hukunci.
Buhari ya sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi.
- An sace Shugaban makaranta a Batsari
- ’Yan bindiga sun kashe Ahmed Gulak
- Buhari ya gana da Jonathan kan rikicin Mali
“Ina mai tabbatar da cewar duk wadanda suke da hannu wajen aikata wannan danyen aiki, ba za su gushe ba tare da an hukunta su ba; Za mu yi amfani da duk wata hanya da muke da ita domin gano su tare da hukunta su daidai da laifin da suka aikata.”
Buhari ya bayyana kisan Gulak a matsayin rashin kishi da kuma kawo wa Najeriya koma-baya.
Ya kuma aike da sakon ta’aziyyarsa ga iyalan Gulak, Gwamnatin Jihar Adamawa, abokan arzikin mamacin da daukacin al’ummar Najeriya.