Kasuwar Hadahadar Hannayen Jari ta Najeriya (NSE) ta yi asarar Naira biliyan 124 a ranar Alhamis.
Sakamakon haka, yawan hannayen jari da ke kasuwar ya ragu zuwa tiriliyan N26.533 daga tiriliyan N26.657 da yake da shi ranar Laraba.
- Yadda muka kama ‘masu daukar nauyin ta’addanci’ a cikin banki a Zariya – Sojoji
- NAJERIYA A YAU: Halin da ’yan gudun hijirar Bama ke ciki bayan komawa garinsu
Hannayen jarin kamfanoni 13 sun fadi, a yayin da wasu 10 suka tashi.
Ga bayanin kamfanoni biyar da hannayen jarinsu suka fi dagawa, da wadanda nasu suka fi yin kasa a kasuwar a ranar Alhamis.
Manyan wadanda suka ci riba su ne:
- Trans-Nationwide; Ribar 8.70% a kan hannun jari daya 75k.
- NEM Insurance; Ribar 2.67% a kan kowane hannun jari N5.39.
- Cutix; Ribar 2.50% kowane hannun jari N2.05.
- Academy Press; Ribar 2.41 a kowane hannun jari N1.70.
- International Breweries; Ribar 2.02% a kan kowane hannun jari N5.05.
Manyan wadanda suka yi asara:
- Conerstone; asarar 10% a kan kowane hannun jari 54k.
- Multiverse Mining and Exploration; asara 9.96%, hannun jari N2.82.
- Cadbury Nigeria; asarar 9.62, hannun jari N2.82.
- BUA Cement; faduwar 6.18%, hannun jari N50.10 per share.
- Guinness Nigeria; faduwar 5.50%, hannun jari N83.
Wadanda suka fi samun ciniki:
Kamfanin NGX Group shi ne ya fi samun ciniki, inda ya rasa hannayen jarinsa miliyan 30.75 da aka sayar a kan Naira miliyan 553.54 million.
Mai bi masa shi ne Zenith Bank da ya sayar da hajar miliyan N24.39 a kan miliyan N488.01.
Fidelity Bank ya sayar da hannayen jari na miliyan 13.84 a kan miliyan N50.66.
First Bank ya sayar da hannun jari na miliyan N11.03 kan miliyan N110.81.
Access Holdings ya sayar a hannayen jari na miliyan N8.23 kan miliyan N68.21.
Gaba daya, hannayen jari miliyan 126.84 da kudinsu ya kai biliyan N1.78 ne aka yi musaya, a hadahda 3,117.
A ranar Laraba kuwa, hannayen jari miliyan 51.88 da kudinsu ya kai biliyan N590.01 aka cefanar.