Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya na kara cigaba, duk da wasu marasa kishi na yunkurin kawo wa zaman lafiyarta tarnaki.
Shugaban ya bayyana hakan ne a sakonsa na bikin Kirsimeti da ya yi ranar Asabar.
- Kirsimeti: Mun yi shirin ko-ta-kwana a Gombe — ’Yan sanda
- Mai sana’ar zanen da ya mai da jininsa tawadar zane-zane
“Wannan ne bikin Kirsimeti na karshe da zan gani a matsayin shugaban kasa.
“Kuma dama ce ta nunawa sauran kasashen duniya cewa lallai Najeriya a shirye take ta tabbatar da tsarin dimokuradiyya kamar yadda ake gani a sauran kasashen da suka cigaba.
“Muna fatan zaman lafiyar da farin cikin da ke tattare da wannan lokaci zai ci gaba har zuwa sabuwar shekara da babban zaben da za a yi a watan Fabrairun 2023 da kuma bayan haka.
“Ina mai tabbatar wa ’yan Najeriya cewa masu neman kawo cikas ga zaman lafiyar da muke ciki tuni muka samu nasara akansu.
“Kasarmu cike take da albarkatun kasa da arzikin yawan al’umma.
“Mu taru mu yi murna da farin ciki da zuwan wannan lokaci, da kuma fatan cewakasarmu za ta zarce haka nan gaba,” inji shi.