Shugaban Kungiyar Masu Hakar Ma’adinai ta Najeriya (MAN), Kabir Kankara, ya bayyana cewa masu hakar ma’adinan ba su da wata alaka da ’yan bindiga.
Kankara ya bayyana hakan ne a bayaninsa kan haramcin da Gwamnatin Tarayya ta sa kan ayyukan hakar ma’adanai a Zamfara sakamakon karuwar ayyukan ’yan ta’adda.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 50 a Zamfara
- Abin da mahaifina ya fada min a hannun ’yan bindiga —Dalibar da aka sako
- Zamfara: Zan yi murabus idan za a samu zaman lafiya —Matawalle
“A iya sanina, mambobinmu ba su da wata alaka da ’yan bindiga kuma muna goyon bayan matakin na Gwamnatin Tarayya don dakile rashin tsaro a Zamfara.
“Tabbas ayyukanmu na hakar ma’adanai suna gudana ne a cikin daji amma ba mu da wata alaka da ’yan fashi, mu dai muna cikin wadanda lamarin ya shafa ne,” inji shi.
Kankara ya ce matakin magance matsalar rashin tsaro a jihar ya yi daidai domin kare lafiya da rayuka da dukiyoyi.
A ranar Talata Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ayyukan hakar ma’adanai da kuma tashin jirage a Zamfara.