✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa sun sace babban jami’in dan sanda a Kebbi

Lamarin ya faru ne a lokacin da jami’in dan sandan ke tafiya tare da iyalinsa cikin mota.

Wani babban jami’in dan sanda mai kula da yanki, wato “Area Commander” ACP Abdullahi Umar Kamba ya fada hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Kebbi.

Lamarin ya faru ne ranar Alhamis da dare a kauyenTashar Rogo da ke kusa da garin Yauri, a lokacin da jami’in dan sandan ke tafiya tare da iyalinsa cikin mota.

Wani na kusa da jami’in da aka sace ya shaida wa Muryar Amurka cewa, ACP Abdullahi ya tabbatar masa halin da yake ciki ta waya ranar Juma’a da safe, amma masu garkuwar ba su tafi da matarsa ba.

Nan take dai rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi ba ta ce komai ba game da batun.

Matsalar tsaro na ci gaba da hana jama’a barci da ido biyu rufe, duk da cewa rahotanni na nuna jami’an tsaro na samun galaba akan ‘yan ta’adda a wasu wurare.