Wani dan sanda mai muƙamin Sajan ya shiga hannu kan zargin harbe mahaifinsa har lahira a garin Maiduguri na Jihar Borno.
Majiyarmu ta tsaro a jihar ta ce Sajan Sunday Linus Wadzani ya harbe mahaifin nasa ne sakamakon sabanin da suka samu.
“Lamarin ta faru ne da misalin karfe 4.30 na yamma ranar Lahadi, 21 fa watan Yuli, 2024,” a cewar majiyar tamu.
Aminiya ta samu rahoto cewa mahaifin da sandan da ya bindige tsohon dan sanda ne mai muƙamin ASP.
- An kama su kan tono gawar dan maƙwabcinsu domin tsafi
- Matashi ya kashe kakansa da fartanya a Borno
- Matatar Dangote: Ku zo ku saya ku yi yadda kuka ga dama —Dangote ga NNPCL
Wannan lamari ya faru ne a unguwar Modugannari da ke kusa da hedikwatar ’yan sanda ta jihar.
Majiyarmu ta ce Sajan din da ke aiki a Majalisar Dokokin Jihar Borno ya shiga hannu, inda ake tsare da shi a ofishin ’yan sanda na unguwar GRA.
Kokarin wakilinmu na samun karin bayani kan lamarin bai yi nasara ba, zuwa lokacin da muka kammala wannan labari.