Dan uwan Ba’amurken nan manomi da aka yi garkuwa da shi a ya ce sai da suka bayar da kudi da burodi gabanin a sako dan uwan nasu daga hannun masu garkuwa.
Mutumin, mai suna Moshood Adebayo, ya ce masu garkuwa da mutanen wadanda daga bisani suka karbi N5m maimakon N100m da suka bukata tun da farko, sun nemi da su zo musu da burodi da lemon kwalba kafin su saki manomin.
- Rikicin IPOB: ’Yan kasuwar Kano sun tafka asarar N77m
- Real Madrid ta sake daukar Ancelotti a matsayin sabon Koci
Ya ce, “An kira ni da misalin karfe 11 na daren ranar Talata, sun ce in kai musu N5m da kwalaben Koka-kola guda uku masu sanyi da burodi sinki biyar; sannan in ajiye musu a kan hanyar Shao zuwa Jebba.
“A Kan hanyar, mun ga shingen sojoji, na tsorata matuka cewa za su tambaye ni ina zan je da wadannan makudan kudaden; wanda ba zan iya ce musu na masu garkuwa da mutane ba ne.
“Na kira inda na sanar da su hakan, sun ce kar na damu.
“Kafin mu isa mahadar Shao, sai suka yi mana nuni da hasken cocila.
“Daga nan suka mana zagi muka yi tattaki zuwa wurin da suka ajiye dan uwan namu [Muritala],” inji shi.
Muritala wanda dan yankin Ile Olosan (Shagaya) ne, a unguwar Apomu, cikin Ilorin, an sace shi ne dai a Pampo, cikin Karamar Hukumar Asa ta Jihar Kwara lokacin da yake tsaka da gewayar gonarsa.
Sace manomin ya shiga jerin mutanen da suka fada komar masu garkuwa da ke kara yawaita a jihar, musamman ma a yankin na Asa.