Wadanda suka yi garkuwa da mutum 14 a kauyen Janjala da ke Karamar Hukumar Kagarkon Jihar Kaduna sun bukaci ’yan uwan wadanda suka sace su kai musu sabbin babura guda biyu da kayan abinci a matsayin fansa.
Sun kuma bukaci a hada musu da kwayoyi da kuma barasa matukar ana so su saki mutanen.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’yan Najeriya suka karbi karin wa’adin tsoffin kudade
- Miyetti Allah ta yi Allah wadai da Gwamnatin Tarayya kan kisan makiyaya a Nasarawa
Aminiya ta rawaito cewa maharan sun sako uku daga cikin mutanen da suka sace a kauyen Kadara da ke makwabtaka da Janjalar, bayan sun karbi kayan abinci da kwayoyi, a madadin sabbin kudin da suka ki karba tun da farko.
Sun ce dai ba za su saki mutanen ba har sai an kai musu Naira miliyan 30 na sabbin kudi.
Da yake zantawa da wakilinmu ta wayar salula a ranar Lahadi, Sakataren Dagacin Janjala, Babangida Usman, ya ce masu garkuwar sun ce musu tun da samun sabbin kudaden na Naira miliyan 14 ya yi wahala, a samo musu baburan da kayan abinci.
“Halin da ’yan uwan mutanen suke ciki ke nan. Yanzu kuma yadda za a sami kudin da za a sayi wadannan kayayyakin ita ce babbar matsala,” in ji Babangida.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ba ta magantu ba a kan lamarin.