✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa na neman miliyan 50 a kan Kansilar da suka sace

’Yan bindigar sun ce idan ba a ba su kudin da suka bukata ba za su halaka ta

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da wata kansila a garin Ogu-Bolo na Jihar Ribas, Hannah Alasomuka na neman Naira miliyan 50 daga iyalanta a matsayin kudin fansar ta.

Hannah, wacce ita ce ke wakiltar Mazabar Ikpokiri ta shida a Karamar Hukumar Ogu/Bolo, wasu ’yan bindiga uku ne suka sace ta bayan tarwatsa mazauna yankin.

Wata majiya ta ce kansilar, wacce aka fi sani da ‘Nurse’ an sace ta ne dab da gabar ruwa ta Igbokiri da ke Jihar.

Daya daga cikin iyalan kansilar, kuma Bulaliyar Majalisar Dokoki ta Jihar, Evans Bipi a wani rubutaccen sako a ranar Talata ya ce masu garkuwar sun bukaci a basu miliyan N50 a matsayin kudin fansar ta.

“Tabbas, lamarin ya faru ne ranar Lahadi da misalin karfe 12 na dare a Ikpokiri, dab da gabar ruwa. Sun bukaci a ba su Naira miliyan 50 ko kuma su kashe ta,” inji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar, Nnamdi Omoni ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa, “Gaskiya ne, mun samu labarin faruwar lamarin. Muna iya bakin kokarinmu wajen kubutar da ita.

“Tuni muka baza jami’anmu domin tabbatar da an kubutar da ita daga hannun su,” inji kakakin.