’Yan bindigar da suka yi garkuwa da wani malamin addinin Kirista a garin Chawai na Karamar Hukumar Kauru da ke Jihar Kaduna, Rabaran Joseph Danjuma Shekari, sun bukaci a ba su Naira miliyan 60 a matsayin fansarsa.
A ranar Lahadi da daddare ne dai wasu masu garkuwa da mutane suka dira gidan Rabaran din inda suka yi awon gaba da shi tare da kashe hadiminsa mai suna Sati Musa.
- Ronaldo ya zama mutum na farko da ya samu mabiya miliyan 400 a Instagram
- Mayakan ISWAP 104 sun mika wuya ga sojoji a Borno
Sati Musa, mai kimanin shekara 20 dalibi ne a makarantar Sakandirin St. Monica da ke Ikulu-Pari a Chawai kuma yana gab da rubuta jarabawa kammala babbar sakandiri ta WAEC ne kafin ya gamu da azal din.
Wata majiya daga garin na Chawai da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya cewa da safiyar Litinin ne masu garkuwar suka kira lambar wayar malamin, sannan suka bukaci a ba su adadin kudin kafin su sako shi.
Darikar Katolika dai ta tabbatar da sace Rabaran din.
A cikin takardar sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun shugaban darikar na shiyyar Kafanchan, Bishop Emmanuel Okechukwu, kungiyar ta tabbatar da yin garkuwa da malamin, inda suka ce an kama shine da misalin karfe 11:30 na daren Lahadi.
“Muna kira ga jama’a da su taya mu addu’a Allah ya kwato shi kuma a guji daukar doka a hannu,” inji sanarwar.