’Yan bindiga na namen a ba su Naira miliyan 200 a matsin kudin fansa bayan sun sace mutum 45 a kauyen Kasuwar Magani da ke Jihar Kaduna.
Maharan sun far wa garin ne tare da kame kimanin mutum 60 ciki har da mata da tsofaffi da kananan yara da marasa lafiya, amma daga baya suka tisa keyar 45 daga cikinsu.
- ‘Yajin aikin ASUU ya karya harkokin kasuwancinmu’
- An kama mushen dabbobi a mayankar Kano
- NAJERIYA A YAU: Irin Asarar Da Cin Ganda Ke Janyo Wa Tattalin Arzikin Najeriya
Kungiyar Al’ummar Kudancin Kaduna (SOKAPU), a cikin wata sanarwa ta ce, a ranakun Litinin da Talata da suka gabata ne ’yan bindigar suka kai hari a kauyen Unguwar Fada da garin Kasuwar Magani da ke Karamar Hukumar Kajuru ta jihar.
“Sun shiga cocin a lokacin da ake tsaka da ibadar dare ranar Talata 13 g watan Agusta 2022 suka yi awon gaba da mutum sama da 60 daga cocin da gidajen da ke makwabtaka da shi.
“Amma ba su iya tafiya da mutanen baki daya ba saboda a cikin mutanen akwai kananan yara da tsofaffi da masu fama da rashin lafiya,” in ji kungiyar.
Sanarwar ta ce maharan sun kuma yi sace mutum biyu a kauyen Janwuriya da ke kusa da Kasuwan Magani, “yanzu haka mutum 45 ne aka zaton suna hannunsu.”
Ta ce masu garkuwa da mutanen sun kira iyalan mutanen a ranar 18 ga watan Agusta suna neman kudin fansa Naira miliyan 200, suna masu cewa mutum 40 ne a hannunsu.
“Yanzu ba a san inda sauran mutanen suke ba; A kananan hukumomin Kajuru da Chikun kuma ’yan bindiga sun mamaye mutane kauyuka inda suka mayar da mazauna tamkar bayi.
SOKAPU, ta bayyanan jajenta ga mazauna da al’ummar Fulani makiyaya da ke yankin wadanda harin ya shafa.
Kugiyar ta jinjina wa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’ar yankin.