✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa da mutane sun yi rantsuwar tuba a Oyo

Wadansu matasan Fulani da Yarabawa da ’yan kasar Togo su 16 sun yi rantsuwar tuba daga barin miyagun ayyuka da suka hada da garkuwa da …

Wadansu matasan Fulani da Yarabawa da ’yan kasar Togo su 16 sun yi rantsuwar tuba daga barin miyagun ayyuka da suka hada da garkuwa da  mutane da satar shanu da fashi da makami da suke yi  a sassan Najeriya.
Bayan sun rantse da Alkur’ani da Baibul cewa ba za su sake komawa ga aikata miyagun ayyukan a rayuwarsu ba, sun kuma yi alkawarin bayar da muhimman bayanan da za su kai ga gano maboyar abokan aika-aikarsu.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen Jihar Oyo, Alhaji Yakubu Bello da hadin gwiwar shugaban kungiyar a karamar Hukumar Borgu a Jihar Kwara, Malam Jiji Umar ne suka jagoranci taron wanke tubabbun matasan da aka gudanar a fadar Aseyin da ke garin Iseyin a ranar Asabar da ta wuce.
Wakilinmu ya zanta da shugabannin da suke tare da daya daga cikin tubabbun da suka ziyarci ofishin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo domin tattauna yadda za a mika makaman da aka samu a hannun tubabbun ga jami’an tsaro. “Mun shirya taron Iseyin ne domin kaddamar da kungiyar ’yan banga da wayar da kan Fulani makiyaya kan illar miyagun ayyuka na garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da satar shanu da fashi da makami wanda yin haka zai taimaka wajen tabbatar da tsaron lafiyar jama’a da dukiyoyinsu a Jihar Oyo da kasa baki daya. kungiyar Miyetti Allah ta samu nasara kwarai domin akwai matasa da yawa da suka tuba suka kawo kansu tare da mika makaman da ke hannunsu. Kuma akwai  wadansu sojoji da ke aikata miyagun ayyuka da kungiyar ’yan banga ta kamo su tana shirin mika su ga ’yan sanda,” inji shugaban na Miyatti Allah.
Shi ma Malam Jiji Umar cewa ya y:i “kungiyar Miyetti Allah reshen Jihar Oyo ta samu labarin ayyukan da muka yi a wasu jihohin Arewa ne na kama masu garkuwa da mutane da satar shanu da ’yan fashi da makami, shi ne ya sa suka gayyace ni domin bayar da shawara kan yaddaza  a kawo karshen wannan lamari a jihar. Alhamdu lillahi, mun zo kuma mun ba su shawarar da ta kai ga kama mutane da yawa daga cikinsu. Musulmi daga cikinsu suna daukar Alkur’ani su dora a  kansu su ce sun tuba. Idan sun mika mana makaman da ke hannunsu sai mu amince da tubarsu.”
dangwaggo Usman yana daga cikin tubabbun, ya ce: “Ina daga cikin masu yin fashi da makami shekara 9 da suka wuce amma ba garkuwa da mutane ko satar shanu. An taba kama ni da aka kawo ni gidan yari na Agodi da ke Ibadan, inda na dade a tsare. Da aka sallame ni sai na ga cewa akwai wahalar gaske a cikin aikin da nake yi, shi ne dalilin da ya sa na tuba kuma na mika kaina ga ’yan banga. A daidai lokacin ’yan bangan suka ki amincewa da tubar da na yi da baki, suka ce dole ne a yi tubar da Alkur’ani kuma a gaban jama’a. Shi ne ya sa na mika kaina a wajen taron na Iseyin na dauki Alkur’ani na dora a kaina, sannan na yi rantsuwar cewa, idan Allah Ya yarda ba zan sake komawa ga aikata fashi da makami ko wani mugun aiki ba. Kuma na yi alkawarin zan rika bayar da labarai ga ’yan banga da jami’an tsaro da za su taimaka wajen kama wadanda suka ki barin wannan mugun hali.”