✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu garkuwa da mutane sun tsare shi suna zukar jininsa suna sayarwa

Sun rika dibar jinin mutumin suna sayarwa a kowanne wata

Wani dan kasar China ya yi ikirarin cewa, wani gungun masu aikata laifuka ne suka sace shi, inda mambobin suke yin amfani da shi kamar “bawan da ake sayar da jininsa.” Suna zujar jininsa a kai-a kai suna sayarwa a kasuwar bayan fage.

Rahotanni daga kasar na bayyana cewa, an sace mutane tare da cire sassan jikinsu, amma wani mutum mai shekara 31 daga birnin Beijing ya yi ikirarin cewa, masu garkuwa da mutanen sun fi sha’awar jininsa.

Mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba, don kare sirrinsa, ya kasance yana aiki a matsayin mai gadi a Beijing da Shenzhen, amma ya yanke shawarar
gwada sa’arsa a matsayin mai gadin gidan rawa bayan ya samu gurbin aiki ta yanar gizo da aka tallata.

Saboda albashin yana da kyau, don haka ya yanke shawarar tafiya zuwa yankin Kudu maso Yammacin Guangxi don tattaunawa ba tare da sanin cewa, gurbin aikin tarko ne ba.

Wasu ’yan jungiyar masu aikata laifuka ne suka yi garkuwa da mutumin lokacin da ya isa Guanxi, inda aka yi safararsa
zuwa birnin Sihanoukville da ke gabar tekun Cambodia ta Vietnam, inda aka yi zargin sayar da shi ga wani gungun
’yan kungiyar a kan Dalar Amurka 18,500, daidai da Naira miliyan 7 da dubu 694 da 150.

An tilasta masa ya aiwatar da tsare-tsare daban-daban na yaudarar talla a waya domin ya samu nasa kudin fansar, sannan kuma ya rika barin ’yan
kungiyar su riia kwasar jininsa akai-akai, don su sayar da shi don riba.

A cewar wasu majiyoyi a China, ana zujar jinin mutumin da ya kai adadin mil 800ml a kowane wata, tun daga watan
Agustan shekarar bara, kuma hannunsa duk ya nuna tabon dibar jinin don tabbatar da hakan, a lokacin da aka ceto shi.

A bayyane yake, masu laifi sun fara dibar jini daga jijiyoyin da ke kansa, bayan wadanda ke hannunsa da kafafunsa sun zama marasa amfani.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta Amurka ta ba da shawarar kada a rika ba da gudunmawar jini akai-akai fiye da kowane kwana 56, amma tawagar masu laifin ta yi watsi da batun inda take zukar jinin mutumin kowane wata.

Har ma sun yi barazanar sayar da sassan jikinsa a kasuwar bayan fage, idan bai ba su hadin kai ba.

Mutumin dai ya samu kubuta daga masu garkuwan da shi ne lokacin da daya daga cikin tawagar ya sauya sheka.

Ya yi nasarar mayar da kansa kasar China, inda a karshe aka kai shi wani asibiti don samun raunin gabobi da yawa, saboda yawan zukar jininsa akai-akai.

Mutumin da ya kubuta da aka yi garkuwan da shi ya shaidawa hukumomi cewa, akwai akalla wasu mutum bakwai da tawagar ke tsare da su, amma ba a daukar jininsu akai-akai kamar yadda aka yi masa ba.

A bayyane yake, yana da nau’in jini na rukunin O, wanda yake kowa na bukata
a duniya, kuma ya fi daraja a kasuwar bayan fage.

Wannan labari mai ban mamaki ya dade yana ta yawo a shafukan sada zumunta na kasar China a makonnin da suka gabata, kuma hukumomin kasar China sun yi ta yin gargadi ga jama’a da su yi
taka tsan-tsan kan tayin aikin Cambodia wanda yake kama da na gaskiya ne amma na bogi, kuma kawai ana yin amfani da hanyoyin sadarwa na zamani wajen neman aikin.