A ranar Litinin din da ta gabata ne da misalin karfe 7:45 wadansu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kashe wani dan sanda mai mukamin saje da yake aikin bayar da kariya lokacin da suke yunkurin sace wani Bature dan kasar Jamus a kan titin Madobi da ke Jihar Kano.
Lamarin ya faru ne a lokacin da Bajamushen Injiniya Michael Cremza da ke aiki da Kamfanin dantata and Sawoe yake duba aikin da kamfanin ke gudanarwa a kan titin Madobi.
Shaidu sun ce ’yan bindigar sun je ne a cikin wata bakar mota kirar Golf inda suka fito suka fara harbe-harbe a kan motar da dan sandan da ke bayar da kariya ga Baturen ke ciki, lamarin da ya sa ya ce ga garinku nan.
“Bayan harbe dan sandan ne sai suka dawo kan Bajmushen suka ja shi suka tura cikin motarsu suka bar wurin suna harbi a sama,” inji majiyarmu.
Wata takarda da Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano dauke da sa hannun Kakakinta SP Magaji Musa Majiya ta ce ’yan bindigar sun bude wuta ne a kan motar da dan sandan ke ciki daga baya suka sace Bajamushen.
SP Magaji Majiya ya ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Rabi’u Yusuf ya hada wani babban rukuni na ’yan sanda wadanda aka baza su yankin da lamarin ya faru don samun nasarar kama wadanda suka yi aika-aika tare da kubutar da Bajamushen.
Rundunar ta yi kira ga jama’a cewa duk wanda yake da wani labari game da lamarin ya sanar da ofishin ’yan sanda mafi kusa.