✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa da mutane sun nemi yin sulhu da gwamnati a Katsina

Masu satar shanu da garkuwa da mutane tare da yin kisan babu gaira babu dalili da suka addabi wasu yankuna a dajin Birnin Gwari a…

Masu satar shanu da garkuwa da mutane tare da yin kisan babu gaira babu dalili da suka addabi wasu yankuna a dajin Birnin Gwari a Jihar Kaduna da kuma kananan hukumomin Sabuwa da Dandume da Faskari zuwa Karamar hukumar Jibiya a Jihar Katsina, musamman kauyukan da ke kusa da Dajin Rugu da ya fada Jihar Zamfara da Sakkwato ya shiga Jamhuriyar Nijar, sun nemi yin sasanci da gwamnatin Jihar Katsina domin kawo karshen ayyukan ta’addancin da suke yi wanda yanzu ya fi yawa a Jihar Katsina.

Jaridar People’s Daily, wadda wakilinka ke cikin wadanda aka gayyata a taron neman sulhun ta ce, babban jagoran ’yan ta’addan da suka addabi Kudancin Jihar mai suna Alhaji Idris Miyaya wanda kuma shi ya jagoranci zaman da aka yi a karshen makon jiya a kauyen Dankolo da ke Karamar hukumar Dandume ya ce, “Mu kanmu mun gaji da wannan zubar da jini a wannan yanki babu wani dalili. Tabbas, babu abin da ya fi zaman lafiya dadi a rayuwar duniya. Saboda haka mun kudiri aniyar ajiye makamanmu don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da dawo da mutuntakar da ke tsakanin Hausawa da Fulani wacce muka rasa a yanzu.”

Miyaya ya kara da cewa, “A lokacin baya da aka yi sasanci da mu, gaskiyar lamari ba dukkanmu ne aka gayyato yayin gudanar da sulhun ba, an dai tattaro wadansu daga cikinmu ne suka halarci taron saboda mun rabu kashi-kashi, shi ya sa wadancan da ba a gayyato  ba suka ci gaba da ayyukan ta’addancin tun daga wancan lokacin zuwa yau. Sai kuma daga cikin wadanda suka halarci taron irin su Baharin Daji sun koma kan danyen aikinsu. Amma a yanzu muna bukatar gwamnatin jihar nan ta sanya baki a dawo a yi sulhu. Mun yi alkawarin zama lafiya da kowa a fadin wannan yanki.”

Wadanda ake zargi da ayyukan ta’addancin sun bukaci jaridar ta isar da wannan sako nasu na neman sulhun ga gwamnatin Jihar Katsina a karkashin shugabancin Gwamna Masari. Har ila yau,sun nemi ’yan banga ko ’yan sa-kai su tsagaita farautarsu tare da yi musu kisan gilla a kauyuka domin samun wannan zaman lafiya tare kuma da zaman cudanya da juna kamar yadda aka sani a baya.

Wadannan bayanai sun samu ne bayan an kammala taron neman sulhun a kauyen Dungun Ma’azu da ke Karamar Hukumar Sabuwa a Jihar Katsina.

A nasu bangaren, Shugaban ’Yan banga na Karamar Hukumar Dandume, Alhaji Lawal Tsoho Albasu ya ce, “A shirye muke  mu saukaka matakanmu matukar kun ajiye makamanku. Mu ma kamar ku muna bukatar zaman lafiya.”

Shi dai wannan taron neman sulhun daga bangaren barayin shanu, da masu sata da garkuwa da mutane gami da kisan gilla shi ne taro na farko bayan sanya wa dokar hukuncin kisa hannu da gwamnatin jihar Katsina ta yi ga masu satar shanun da garkuwa da mutane tare da hukuncin daurin rai-da-rai bayan biyan diyya da tara.

Aminiya ta nemi jin ra’ayin jama’a a kan wannan lamari, inda baki ya kasu biyu. Wadansu na cewa a bi hanyar sulhun tunda su suka nema abin zai yi tasiri, yayin da wadansu suka nuna cewa ko an yi sulhun babu inda abin zai kai, tunda an yi a baya maimakon a samu sauki sai matsalar ta ci gaba da karuwa.