✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu garkuwa da mutane sun kashe yaro bayan sun karbi kudi

Wadansu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe wani yaro dan shekara 15 da suka sace, bayan sun karbi kudin fansa Naira…

Wadansu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe wani yaro dan shekara 15 da suka sace, bayan sun karbi kudin fansa Naira miliyan biyar da rabi a Bauchi.

Da ya ke zantawa da manema labarai bayan da aka bisne mamacin, mahaifin yaron, Dokta Muhammad Auwal Abubakar Suleiman, ya ce al’amarin ya faru ne ranar Alhamis 2 ga watan Afrilu.

Ya ce ya tafi wajen aiki domin yana cikin likitocin da ke aiki a kwamitin da aka kafa kan yaki da cutar coronavirus jihar Bauchi sai aka kira shi a waya aka ce masa kai ne baban Sadik?

Da ya amsa sai suka ce “mun dauki danka amma in kana son danka ka ba mu Naira miliyan goma ko kuma mu kashe shi”.

Dokta Suleiman ya kara da cewa, “Bayan sun ajiye waya sai na kira iyalina a gida na ce musu ina Sadik yake? Suka ce sun duba ba su gan shi ba, sai na ce to ina zuwa.

“Na bar wajen aiki na koma gida muka duba ba mu gan shi ba.

“Bayan kwana biyu sai suka sake kira na suka ce in ba su Naira miliyan bakwai.

“Suka zo da dare suka karbi wadansu daga cikin kudin a hannu wasu kuma suka karba a cikin asusun banki don sun  ba ni lambar asusun banki guda uku suka ce in sa kudin a ciki, kuma na saka kudin kamar yadda suka bukata, sai suka ce in je kwanar Inkil bayan sallar Magariba in dauki dana.

“Daga baya aka sake kira na ina sallah; da na idar sai suka ce in je wajen wasu majami’u a Kangere in duba zan ga yaron a jikin cocin.

Na je, wasu ’yan uwana su uku suka bi ni muka duba wajen ba mu ga yaron ba. Muka dawo”.

Mahaifin ya ci gaba da bayani a kana bin da ya faru bayan dawowarsu.

“Bayan mun dawo sai ’yan sanda suka kira ni suka ce in je  ofishinsu—domin an kai rahoton bacewarsa wa ’yansanda suma suna nasu aikin.

“Bayan na je suka nuna mini mutane uku suka ce sun kama su kuma sun tabbatar da cewa su ne suka sace yaron, kuma har daya daga cikinsu ya sayi mota Marsandi ta Naira miliyan biyu da dubu dari uku da wayoyi da kudinsu ya kai N160,000 ko wannensu da kuma wasu kayayyaki.

“Kuma sun tabbatar da cewa su ne suka aikata; suka kuma ce akwai wani yaro daya da yake Azare, sai ’yan sanda suka je suka dauko shi”.

Mahaifin yaron ya kuma ce jami’an tsaron sun shaida masa cewa wadanda suka sace wannan yaro sun kasha shi, kuma sun kai ’yansanda wajen da suka binne gawarsa.

“’Yan sandan suka zo suka dauke mu da ’yan uwana muka je wani fili wajen gidan makwabcina inda suka binne gawarsa, muka tona inda suka turbude shi muka dauko shi muka kai asibiti, likita ya duba shi ya ce ya rasu kuma ya lura akwai yanka a wuyansa da kuma bugu mai karfi a kansa”.

Mahaifin yaron ya kuma ce, “Ka san wanda aka zalunta ba abin da zai nema sai adalci saboda haka muna rokon adalci a wajen hukuma don ya zama darasi ga na baya, saboda idan hukuma ba ta dauki mataki a kan wannan ba, Allah ne kadai ya san wanda wannan abu zai shafa a gaba, kuma muna rokon Allah ya bi mana kadi”.

Jami’in hulda da jama’a na Rundunar ’Yan sanda ta jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce an kama wasu daga cikin wadanda ake zargin.

Satar mutane don neman kudin fansa dai ta zama ruwan dare a wasu sassan arewacin Najeriya.

Ko a watan jiya ma, an ba da rahoton sace wani dan uwan gwamnan jihar ta Bauchi, Bala Mohammed, wanda aka sako a makon da ya gabata, ko da yake babu wani bayani a kan ko an biya kudin fansa.