✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa da marayu a Abuja na neman N30m a matsayin kudin fansa

'Yan bindigar sun bukaci a ba su N10m kafin su saki marayun bakwai da mai gadi.

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da marayu bakwai, da mai gadi a yankin Abaji da ke Birnin Tarayya, Abuja, sun bukaci a ba su Naira miliyan 30 a matsayin kudin fansa.

Aminiya ta rawaito a ranar Asabar cewa ’yan bindiga sun shiga gidan marayu na Rachael da ke daura da Makarantar Sakandare ta Naharati, a yankin, suka yi garkuwa da mutum takwas da wasu matan aure uku.

’Yan bindigar sun bukaci a biya N10m kudin fansar marayun da kuma mai gadin gidan marayun.

Har wa yau, sun bukaci N10m a matsayin kudin fansar ragowar mutane ukun: Momoh Jimoh, matarsa Khadija Jimoh, da kuma Rukaiya Salihu, wadanda aka sace a lokacin garkuwa da marayun.

Wata majiya daga gidan marayun da ta bukaci a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu cewa, ’yan bindigar sun bugo waya ranar Lahadi inda suke bukatar N10m ga marayun da kuma mai gadi.

“Ko da yammacin nan sai da suka kira mu a waya suna bukatar N10m kan marayun da mai gadi, amma mun tunatar da su wanda suka yi garkuwar da su marayu ne,” a cewarsa.

 Ba mu da kudi —Gidan marayun

Sai dai a cewar majiyar tamu, Hukumar Gudanarwar gidan marayun ta sanar da su ba ta da wannan kudin, saboda marayun ana ciyar da su da kuma tufatar da su ne da taimakon mutane da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

Ya kara da cewa, “Har barazana suka yi da za su kashe yaran, amma sun nuna musu yaran marayu ne, ba su da uwa balle uba.”

Hukumar gidan marayun, har yanzu ba ta cimma wata matsaya da masu garkuwar ba, amma ya shaida wa wakilinmu cewa sun sanar da jami’an tsaro halin da ake ciki.

Bayan shawarar jami’an tsaro, an kwashe ragowar marayun zuwa cikin Abuja, saboda ci gaba da tsaron rayuwarsu.

Sai dai har yanzu Kakakin ’Yan Sanda na Abuja, ASP Maryam Yusuf, ba ta amsa sakon wayar da wakilinmu ya aike mata ba game da lamarin ba.