✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu garkuwa da mahaifin tsohon Gwamnan Filato sun shiga hannu

Wannan ne karo na biyu da ake sace shi a kauyen na Mushere.

Mambobi shida daga cikin gungun wadanda suka yi garkuwa da mahaifin tsohon Gwamnan Jihar Filato, Joshua Chibi Dariye sun shiga hannu a Karamar Hukumar Bokkos ta Jihar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Ubah Gabriel wanda ya tabbatar da hakan a Jos ranar Lahadi, ya ce an sami nasarar kama su ne a wata maboyarsu bayan wani samame da jami’ansu suka kai.

An dai sace Chibi Dariye ne a watan Yunin 2020 a kauyen Mushere da ke Karamar Hukumar Bokkos da ke Jihar.

Tun lokacin dai ba a san inda yake ba sai a makon da ya wuce da aka gano tare da cafke masu garkuwa da shi.

Rahotanni na nuna cewa wannan ne karo na biyu da ake sace mahaifin tsohon Gwamnan a gidansa da ke kauyen na Mushere

Ko a shekarar 2015 ma sai da aka sace shi kafin daga bisani a sako shi bayan an biya masu garkuwa da shi kudin fansa.