Rundunar ‘yan sandan Jihar Borno ta yi nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargi da ta’adar garkuwa da mutane yayin da suke kokarin karbar kudin fansa a Maiduguri.
ASP Daso Kenneth, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Alhamis a hedikwatar ‘yan sandan da ke Maiduguri.
A cewar ASP Kenneth, ‘yan sanda sun samu rahoto daga wata mai suna Hauwa Audu Adamu da ta bayyana cewa danta mai shekaru 10 mai suna Hisham Mohammed ya bace bayan ya fita sallar Juma’a kuma bai dawo gida ba.
Ta shaida wa ’yan sandan cewa daga bisani wadanda ake zargin sun yi garkuwa da dan nata sun tuntube ta, inda suka bukaci a biya su kudin fansa N3,000,000 domin a sako danta.
Bayanai sun ce a yayin tattaunawar ce masu garkuwar suka rage kudin fansar ya dawo N400,000.
Sai dai ASP Kenneth ya bayyana cewa bayan da ’yan sanda suka shiga lamarin ne suka samu nasarar damke mutanen biyu da ake zargi.
Haka kuma, jami’in dan sandan ya ce sun yi nasarar ceto yaron da abin ya shafa cikin koshin lafiya, yayin da wadanda ake zargin da ke hannu tuni sun amsa laifinsu dangane da garkuwar da suka yi.
A wata hira da manema labarai, Umar Usman, daya daga cikin wadanda ake zargin, ya bayyana cewa sun yi amfani da Keke Napep dinsu wajen sace yaron a lokacin sallar Juma’a a unguwar Sajeri da ke Maiduguri.
Usman ya ce, “Mun ajiye shi a dakina, kuma muka bukaci mahaifiyarsa da ta biya mu Naira miliyan uku.
“Mun tattauna ta lambar wayar mahaifiyar yaron da ya bayar, kuma muka sasanta kan biyan Naira 400,000.
“Sai dai ana tsakar haka ne rundunar ‘yan sandan ta kama mu nan take bayan karbar kudin fansa. Ba mu taba ko kwabo daga cikin kudin ba,” in ji Usman.
Aminiya ta ruwaito cewa, rundunar ’yan sandan ta yi wa manema labarai holen mutanen biyu da sauran wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da barna, kisan kai, hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, da kuma garkuwa da mutane.
Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana jin dadinsa ga al’ummar Jihar Borno kan yadda suke ci gaba da bayar da rahoton abin ki da ya faru cikin gaggawa.
Ya kuma bai wa jama’a tabbacin gudanar da bincike mai zurfi tare da gurfanar da su a gaban kotu a kowane irin yanayi.