Masu garkuwa da mutanen da suka sace tsohon Mataimakin Shugaban Gundumar Kuje ta Abuja, Mohammed Baba, da wasu ma’aikata sun ce sai an ba su Naira miliyan 100 kafin su sako su.
- An sako Basaraken Abuja bayan biyan kudin fansa Naira Miliyan 6.5
- An kashe Mataimakin shugaban Abaji bayan biyan kudin fansa
- An kama wadanda suka yi garkuwa da mai gidansu suka kashe shi bayan sun karbi kudin fansa
Aminiya ta ruwaito cewar, ’yan bindiga sun sace Baba da Kansiloli biyu da wasu mukarraban Shugaban Gundumar ne a kan hanyar Kabbi-Gaube bayan sun dawo daga walimar sabon Sakataren LEA na Gundumar, Yunusa Zakara.
Wani jami’in gundumar ya ce masu garkuwar sun kira wani baban ma’aikacinsu a waya ranar Lahadi, suna neman a kai musu miliyan N100
“Har yanzu ana kan tattaunawa saboda kudin da suka sanya sun yi yawa; Muna son su rage kudin fansar”, inji shi.
Aminiya ta kuma jiyo cewa masu garkuwa da mutanen suna neman kudin fansa Naira miliyan 10 na wani mutum da dansa mai shekara 23 da aka sace ranar Laraba a unguwar Sabon Pegi da ke cikin yankin.
Dan uwan wanda aka sacen ya ce masu garkuwar sun tuntubi iyalan cewa Naira miliyan 10 za a ba da a fanshe su.
Wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Abuja, ASP Mariam Yusuf, inda ta ce rundunar ba ta san masu garkuwar sun nemi kudin fansar ba.
Mariam ta kuma bayyana cewar za su kwato duk wadanda aka sace.