✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu garkuwa da ma’aikacin jami’a a Jigawa na neman N20m

Yan bindigar da suka yi garkuwa da ma'aikacin Jami'ar Jigawa na neman N20m

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da wani ma’aikacin Jami’ar Tarayya dake Dutse (FUD) a jihar Jigawa ranar Alhamis sun bukaci a basu Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansar.

Rahotanni sun nuna cewa an sace Shehu Abdulhamid wanda ma’aikaci ne a asibitin jami’ar lokacin da yake dawowa daga Kano tare da abokansa a daidai hanyar Gaya zuwa Dutse.

Aminiya ta gano cewa Shehun tare da abokan nasa sun bar Kano ne da misalin karfe takwas na dare a ranar da lamarin zai faru, kafin su ci karo da masu garkuwar da suke sanye da kayan sojoji a dab da garin Gaya, wurin da dama ya yi kaurin suna wajen ayyukan fashi da makami.

Kakakin jami’ar ta FUD, wanda ya tabbatar da hakan ya ce ‘yan bindigar sun fidda Shehun daga motar ta karfin tsiya sannan suka umarci abokan tafiyarsa su tafi da motar domin su shaidawa iyalansa abinda ake ciki.

Ya ce masu garkuwar sun bukaci a basu Naira miliyan 20, amma bayan dogon ciniki sun amince su karbi Naira miliyan biyar da rabi kafin su amince su sake shi.

Kakakin ya ce tuni hukumar jami’ar ta sanar da hukumomin ‘yan sanda faruwar lamarin.

To sai dai kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar, Abdul Jinjiri ya ki cewa uffan kan batun, inda ya ce tun da lamarin a Kano ya faru, rundunar can ce mafi zama ahakku ta yi magana a kai.