Wasu mutane da ake zargin masu fasa-kwauri ne sun hallaka wani jami’in Hukumar Hana Fasa-Kwauri ta Kasa (Kwastam) ranar Asabar a yankin Owode da ke Karamar Hukumar Yewa ta Kudu a Jihar Ogun.
Jami’in dai mai mukamin Custom Assistant 1 shi ne direban da ke aiki da Sashen Ayyuka na Musamman na hukumar.
- Luguden wuta ya sa ’yan bindiga sun fara neman sulhu a Zamfara – Matawalle
- Sojoji sun kashe direba ta hanyar lakada masa duka a Jos
Rahotanni sun ce an kashe shi ne yayin wani artabu tsakanin wasu motoci guda biyu da ke makare da shinkafa ’yar kasar waje wadanda aka kama za a tafi da su zuwa Legas.
Kakakin shiyya ta daya na hukumar da ke Legas, Theophilus Duniya ne ya tabbatar da kai harin ga wakilinmu ranar Lahadi, ko da dai bai bayyana sunan jami’in ba.
Duniya ya ce tun da farko dai hukumar ta kama motocin ne inda a yayin yunkurin kai su zuwa Legas daya daga cikinsu ta lalace a kan hanya kuma aka tsaya gyara ta.
A cewarsa, “Ana cikin gyaran ne sai masu fasa-kwaurin suka yo tururuwa dauke da muggan makamai da kayan asiri har suka sami nasarar kashe jami’in namu.
“Yanzu haka mun kai gawarsa zuwa sashen adana gawarwaki a asibiti,” inji shi.
Ya ce tuni mai rikon mukamin babban kwaturolan hukumar na shiyya ta daya ya bayar da umarnin a gaggauta fara binciken musabbabin kisan.
Kakakin ya kuma ce kwanturolan ya yi Allah-wadai da kisan inda ya ce hakan ba zai sa su yi kasa a gwiwa ba kan yakin da hukumar ke yi da masu fasa-kwauri.