✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu fasa-kwabrin fetur sun sha luguden wuta

A ƙarshen makon jiya ne rundunar sojin sama ta  Najeriya ta yi luguden wuta a kan  tsagerun nan da suka addabi al’ummar yankin Arepo da…

A ƙarshen makon jiya ne rundunar sojin sama ta  Najeriya ta yi luguden wuta a kan  tsagerun nan da suka addabi al’ummar yankin Arepo da Ibafo a Jihar Ogun da wasu sassan karamar Hukumar Ikorodu a Legas, ɓarin wutar da ya ɗauki hankulan mutane da dama a kurmi da ma ɗaukacin ƙasa baki ɗaya. Bayan da rundunar sojin ta fitar da wani faifan bidiyon da yake nuni da irin atisayen da shawagin da sojin saman suka yi a yankin.
Babban jami’in ’yan sanda da ke kula da shiya ta biyu wacce ta ƙunshi jihohin Legas da Ogun,  Abdulmajid Ali ya shaida wa Aminiya cewa, jami’an tsaron haɗin gwiwa waɗanda suka haɗa da sojin sama da na ruwa da na ƙasa da rundunar ’yan sanda da jami’an tsaro na farin kaya ne suka yi ɓarin wuta a kan tsagerun, waɗanda suka addabi al’ummar yankin.  
“Mutane na kiran su tsagerun Nejar-Dalta, mu ba a haka muke ganin su ba, wasu tsageru ne da ke ayyukan ta’addanci, waɗanda suka haɗa  da fasakwaurin manfetur da fyaɗe da yin garkuwa da jama’a da fasa bututun manfetur. Don haka irin wannan luguden  wuta shi ya cancanta a kan su daman  tun a baya can muna yin farautar su,” inji shi.
Abdulmajid Ali ya ƙara da cewa tsagerun sun ƙunshi al’umma daban-daban ba wai’ yan Neja-Dalta ne kawai ba, kamar yadda ake ta yayatawa.
A cewarsa: “’Yan ta’adda ne da suka haɗa da kabilu da dama. Akwai ’yan Neja-Daltan da Hausawa da Yarbawa da Ibo, a matsayin ɓatagari muka ɗaukesu ba za mu saurara musu ba. Mun kama da yawa daga cikinsu  za kuma mu cigaba da farautar su. A yanzu ƙura ta fara lafawa a yankin, kuma mutanen yankin na cigaba da harkokin su,  jami’an mu na cigaba da yin sintiri,” inji shi.
A ranar Litini ɗin data gabata ne Gwamnan Jihar Ogun Sanata Ibikunle Amusu ya kai ziyarar gani da ido a wuraren da jami’an tsaron suka yi wa luguden wuta, inda ya iske kayayyakin da tsagerun ke amfani da su wajen fasaƙwaurin manfetur, waɗanda  suka haɗa da jiragen  ruwa ƙirar  kwale-kwale da ɗaruruwan jarkokin zuba manfetur. Kuma nan take ya bayar da umarnin ƙone su, gwamnan ya yaba wa Shugaba Buhari bisa kwararan matakan sojin da aka ɗauka a kan tsagerun, ya kuma sha alwashin ci gaba da haɗin gwiwa da gwamnatin tarraya don ganin a kawo ƙarshen miyagun aikace-aikacen baki ɗaya.
Alhaji Salisu Garba Bashankai ɗaya ne daga cikin shugabannin ’yan Arewa waɗanda ke zaune a daura da yankin da tsagerun suka addaba a baya, ya shaida wa Aminiya cewa, matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka a kan tsagerun abin a yaba ne, bisa la’akari da irin ta’addancin da suke shukawa a ’yankin.
“Sun addabi jama’a da sace-sace da yi wa mata fyaɗe da yin garkuwa da mutane, jama’ar yankin a firgice suke ba sa iya fita harkokinsu na yau da kullum. Ai ka ga wannan matakin shi ne zai kawo ƙarshen ta’addacin. Ai dama shi wargi wuri yake samu, wannan ya tabbatar mana da cewa babu wajen wargi a wannan gwamnati ta Shugaba Buhari.  Da a ce tun a gwamnatocin da suka shuɗe irin wannan mataki ake ɗauka a kan tsageru masu tada ƙayar baya da ba a samu wasu masu iƙirarin yin tsageranci ba,” inji shi.