Hukumar Binciken Hatsarin Jiragen Sama (AIB) ta mika rahoton hatsarin jirgin sojin da ya yi ajalin tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Manjo-Janar Ibrahim Attahiru.
A ranar Laraba kwamitin biciken ya mika rahonsa ga Babban Hasfan Sojin Sama, Air Marshal Oladayo Amao, wanda shi ne ya kafa kwamitin na AIB da hadin gwiwar Rundunar domin gano musabbanin hatsarin.
Manjo-Janar Ibrahim Attahiru ya rasu ne tare ’yan tawagarsa mutum 12 a hanyarsu ta halartar bikin yaye kuratan sojoji a Zariya, bayan jirgin samfurin Beechcraft King Air 350i, ya yi hatsari ya kone kurmus, babu wanda ya tsira a cikinsu a ranar 21 ga Mayu, 2021.
A jawabinsu, kakakin rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet, da takwaransa na AIB, Tunji Oketunbi, sun ce rahoton ya kunshi bayanan da aka tattara a yayin binciken, sharhinsu da kuma abubuwan da aka gano da ma shawarwari.
Sanarwar da suka fitar ta ce, “A lura cewa a matakin farko, an gano abubuwa 27 tare da bayar da shawarwari takwas na tsaron lafiya wadanda rundunar da sauran mahukunta za su aiwatar.
“Rahoton zai bayyana abin da ke kunshe cikin na’uarar nadar bayanan jirgin, da tsarin masu kula da shi da kuma sharhin kowannensu.”
Da yake karbar rahoton, shugaban rundunar, ya ce manufar binciken ita ce tabbatar da aminci a sufurin jiragen sama, ba wai kawai a gano mai laifi da kuma hukunta shi ba.
A cewarsa, hadin gwiwar alama ce ta karfi da ingancin da ake bukata a harkar binciken hatsarin jiragen sama da kuma yin komai a fili.
A nasa bangaren, Shuagaban AIB, Injiniya Akin Olateru, ya ce binciken hadin gwiwar shi ne irinsa na farko da AIB ta yi tare da rundunar, kuma na biyu da ta yi tare da wata hukumar soji.
Ya bayyana cewa za a mika kwafin rahoton ga Ministan Sufurin Jiragen Sama da Hukumar Kula da Sufurin Jirage Sama (NCAA) domin ganin an aiwatar da shawarwarin da ke kunshe a ciki.
Ya ce duk da cewa jirgin soji ne, hatsarin ya auku ne a filin jirgin farar hula, kuma hadin gwiwar ta taimaka wajen rufe gibin da ke akwai a bangaren sufin jiragen sama.