✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu amfani da wayar salula sun kai kimanin 139 – NCC

Hukumar NCC ta ce yawan wadanda suke amfani da wayoyin salula sun kai kimanin miliyan 139 a watan Agusta sama da abin da aka samu…

Hukumar NCC ta ce yawan wadanda suke amfani da wayoyin salula sun kai kimanin miliyan 139 a watan Agusta sama da abin da aka samu a watan Yuni wanda ya tsaya a miliyan 138.

Wannan bayanin ya fito ne daga Hukumar NCC a bayananta na wata-wata a shafinta na yanar gizo, inda ta ce an samu ci gaba da 295,685 a watan Agusta.

A bangaren lura da masu amfani da wayoyin (CDMA), an samu masu amfani da wayoyi 217,566 a watan Agusta, wanda ya zama daidai da na Yuli.

Rahoton ya nuna cewa amfani da yanar gizo  wanda ba sai an hada waya ba kai tsaye ya kai 142,478 a watan Agusta da kuma 142,262 a watan Yuli.

Hakanan kuma rahoton ya nuna cewa bangaren (bOIP) na watan Agusta ya kai 56,900, sannan kuma a watan Yuli ya kai 53,297, wanda ya nuna an samu qarin 3,605.

Hadakan wayoyi na watan Agusta ya kai 99.60, na Yuli kuma 99.39, wanda ya nuna an samu qari na 0.21.

Hadakan waya na nufin yadda ake hada wayoyi guda 100 a waje daya. Kuma yana da bambanta a kowane bangare.

Hukumar NCC ta ce layukan da ke aiki a watan Agusta ya kai miliyan 236,603,992, na Yuli kuma ya kai miliyan 237,629,645, wanda ya nuna ragowar 102,565.3.

Yawan masu amfani da yanar gizo wanda ba sai an hada da waya ba kai tsaye ya kai 375,740 a watan Agusta, na watan Yuli kuma ya kai 376.437 wanda ya nuna ragowa na 679.

A cewar Hukumar ta NCC, amfani da murya a yanar gizo (bOIP) ya kai 203,232 a watan Agusta, na Yuli kuma 190,450, wanda ya nuna qaruwa na 12,782.