Wasu daga cikin masoya fitaccen mawaki a masana’antar Kannywood, Nura M. Inuwa, sun yi zanga-zanga kan rashin fitar da sabon kundin wakokinsa a bana, sabanin yadda ya saba yi duk shekara.
Masoyan dai sun yi zanga-zangar ne a ranar Litinin, da misalin karfe 1:30 na rana, inda suka yi tattaki zuwa ofishin mawakin dake kan titin Jami’ar Bayero, dauke da kwalaye.
- An kai daraktan Kannywood Ashiru Nagoma asibiti
- 2020: Muhimman abubuwan da suka faru a Kannywood
- Kotun Musulunci ta sa a kamo mawaki Rarara kan ‘boye matar aure’
Hakan ne ya sa Aminiya tuntubi mawakin ta wayar tarho, inda ya bayyana dalilinsa na rashin fitar sabbin wakokinsa.
Nura ya ce,
“Bayan zuwansu, na fito na kuma ba su hakuri kan rashin fitar wakokina ko sabon kundin waka.
“Tun a baya na sha fadar cewar yanzu zan koma sakin kundin waka duk bayan shekara-shekara.
“Kuma sun fahimce ni tare da yi min uzuri game da sabon salon da na dauka,” in ji Nura.
Masu zanga-zangar, wadanda yawancinsu matasa ne na dauke da kwalaye wanda aka yi rubuce-rubuce a jikinsu.
Bayan zuwansu mawakin ya fito daga ofishinsa, inda ya musu jawabi tare da nuna jin dadinsa game da nuna kulawarsu a gare shi.
Ko a satin da ya gabata, mawakin sai da ya wallafa hotunan sakonnin wasu daga cikin masoyansa, kan yadda suke rokarsa a kan ya buga sabon kundin waka.
‘Masoyana sun kafa tarihi’
Shi ma mawakin ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Instagram, inda yake cewa
“Karon farko a tarihin waka, a 2021 ni da ku mun kafa tarihi.
“Wannan zanga-zanga da kuka yi tana da ma’ana a wurina sosai, ta sani fargaba kuma ta sani farin ciki, saboda da ku na kafu na kai matsayin da ake labartawa,” cewar Nura.
Wasu daga cikinsu sun sa ran mawakin zai saki sabon kundi a watan Janairun 2021.
Amma mawakin ya jima yana ba wa masoyan nasa hakuri kan rashin fitar wani sabon kundin waka daga shi.
Amma a wannan karon ya musu albishir kan cewa nan da wani lokaci kadan zai saki sabon kudin wakokinsa.
Amma ya ce wannan sabon salo da yazo da shi, ya tabbata masoyan nasa za su yi farin ciki da shi.
Nura M. Inuwa, a yanzu ya fi mayar da hankali wajen buga wakokin biki da kuma wanda ake sa wa a cikin fim.