Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya yi kashedi ga makarantun Islamiyyya da na allo da suka bude bayan sassauta dokar kulle a jihar da su gaggauta rufe su.
Gwamna Masari ya ce sassauta dokar bai ba da damar bude makarantu don ci gaba da karatu a cikinsu ba.
Ya kuma jajjada cewa makarantun boko ma za su ci gaba da zama a rufe har sai abin da hali yayi.
Masari ya kuma haramta barace-barace a fadin Jahar tare da umartan jami’an tsaro su kama duk almajirin da ke gararambar bara da kuma wanda almajirin ke hannunsa domin hukunta shi.
- An bude kasuwanni, za a koma aikin gwamnati a Katsina
- An nada dan NYSC sabon Hakimin Yantumaki
- Ku ragargaza ‘yan bindigar da suka addabi Katsina – Sadique
Ya yi jawabin ne bayan taronsa da malaman addini, jami’an tsaro, kwamitin cutar coronavirus da sauran masu ruwa da tsaki domin yin bitar abubuwan da suka faru da cutar ta COVID-19.
Masari ya sake kira ga jama’a da su ci gaba da kiyaye dokoki da shawarwarin masana lafiya domin hada yaduwar cutar coronavirus musamman ta yin amfani da kyallen rufe fuska da kuma bayar da tazara a tsakanin taron jama’a.