Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya haramta ayyukan kungiyar ’Yan Sa-Kai a fadin jihar baki daya ba tare da wani bata lokaci ba.
Cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan jihar shawara ta musamman kan harkokin tsaro, Ibrahim Ahmad ya sanya wa hannu, gwamnatin ta ce da wannan sanarwa ta umarci ’yan sanda da sauran jami’an tsaro su rushe wannan kungiya ta ‘Yan Sa Kai a duk fadin jihar.
- NAJERIYA A YAU: Abin da Abba Kyari Ya Fada Kafin A Kama Shi
- Senegal za ta sanya wa filin wasa sunan Sadio Mane
Sanarwar da gwamnatin ta fitar a Yammacin Litinin ta ce ta yi hakan ne bisa la’akari da azarbabin da ’yan kungiyar ke yi wajen aikata miyagun laifuka, da hakan ke kai su ga kisan gilla a kan mutanen da ba su ji ba ba su kuma gani ba, tare da kwashe musu kaya da sunan aikin tsaro na ‘Yan Sa-Kai.
Sanarwar ta ce daga yanzu gwamnatin jihar ta amince ne kawai da kungiyar ’yan sintiri ta Vigilante Group, wadda ke karkashin kulawa da saidon ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da kuma hukumomin gargajiya.
Gwamnatin ta ce daga yanzu ba a yarda kowa ya zartar da wani hukunci da doka ce kawai ya kamata ta yi ba, bisa kowane dalili, illa duk wanda aka kama bisa zargin aikata wani laifi a mika shi ga ’yan sanda ko wata hukumar tsaro domin daukar matakin da ya dace, idan har akwai bukatar hakan.