Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bukaci ’yan Najeriya da su dage wajen yi wa zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu addu’a.
Masari ya bayyana haka ne wajen taron buda baki na musamman da aka shirya gidan gwamnatin Katsina, inda ya gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya sanya aka yi zabe lafiya.
- Kano: Ba zan rika yi wa gwamnatin Abba katsa-landan ba – Kwankwaso
- Mamallakin Manchester City ya zama Mataimakin Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa
A cewar gwamnan, zababben shugaban kasar, yana gudanar da taron addu’a na musamman duk shekara a watan Ramadan.
Ya ce: “Taron wannan shekarar an shirya shi don gode wa Allah kan nasarar da aka samu a zaben da ya gudana a fadin kasar nan.
“Ba abin da za mu yi face mu gode wa Allah kan nasarar da muka samu a Katsina da Najeriya.
“Wannan shi ne babban dalilin da ya sa muka hadu da shugabannin Addini, shugabannin gargajiya, ma’aikatan gwamnati da masu ruwa da tsaki.
“Akwai sabon shugaban kasa da aka zaba, yana bukatar addu’a, abu mafi muhimmanci shi ne mutane sun gane bayan zaben shugabanni suna kuma bukatar addu’a.”