Lamidon Adamawa, Dokta Barkindo Aliyu Mustapha ya ce an bude gidan rediyon Pulaaku FM ne don bunkasa al’adunsu da kuma yaren Fulfulde a Afirka baki daya.
Lamidon ya bayyana hakan ne a wata taron da aka yi na sanya daraktoci na wannan gidan rediyon Pulaaku FM a inda ya ce rediyon zai fara aiki a Jihar.
Lamidon wanda shi ne ya kawo wannan tsari na bude gidan rediyon ya ce bayan labarai da ‘yan Adamawa za su rika sauraro a tashar, za a rika kawo musu ababen al’adu domin inganta ilimin jama’a.
Lamidon wanda ya kasance shi ne shugaban kungiyar Tabital Pulaaku na Fulani da ke Afrika ta yamma da ta tsakiya, ya bayyana cewa labaren da za a rika kawowa a tashar za a rika kawo su ne da harsunan fulatanci da hausa da kuma turanci domin sanya masu sauraro su ji labarai a kasar baki daya.
Ya ce “Harshen Fulfude wadda shi ne ainihin harshen jihar, ba a amfani da shi sosai kamar yadda ya kamata a tsakanin fulanin. Dalilin hakan ne ya sanya muka kawo rediyon Pulaaku FM domin taimakawa jama’ar jihar wajen kawo musu labarai masu kayatarwa da inganci da harshen da suke ji”. Inji shi.
Ya kara da cewa “Anfi amfani da turanci da hausa da kuma fulatanci a wannan bangaren na mu, musamman a gidajen rediyo shi ya sa muka ce bari mu fito mu kawo gidan rediyon da zai inganta al’adarmu da ilmantar da jama’a game da al’adunmu da kuma sauraron kade kade na yaren fulatanci irin wanda aka sanmu da su”. Inji shi.
Gwamnar Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya halarci wannan taron kuma ya nuna farin cikinsa domin kawo irin tsarin wannan gidan rediyon a jihar da kasar da kuma Afirka baki daya.
Ganduje ya umurci daraktocin da aka sanya da kuma sabbin ma’aikatan da su hada kansu domin kawo shirye shirye masu gamsar da jama’a wadanda za su kawo kwanciyar hankali a tsakanin jama’a.
Hakanan kuma ya umurci mutanen Jihar Adamawa da su kasance ma su yin amfani da yaransu domin taimakawa yaren kada ya bata.
A na shi bangaren, gwamnan Jihar Adamawa, Muhammadu Umaru Jibrilla Bindow cewa ya yi lallai gidan rediyon Pulaaku zai taimaka sosai wajen gyara rayuwar mutanen cikin jihar.
Ya kara da cewa gidan rediyon zai taimaka sosai wajen sanar da mutanen da ke kauyuka sanin lokacin da za su yi rajistan zabe da kuma yadda za su sami katin zabensu da na kasa.
Mataimakin gwamnan Jihar Adamawa Inginiya Martins Babale wadda ya wakilci gwamna ya ce gidan rediyon zai taimaka wajen yada labarai masu ma’ana da ilmantarwa da kuma nishadantarwa ga jama’a.
Binciken Aminiya ya gano cewa ‘Pulaaku’ na nufin kunya da hakuri da kuma kirki.