✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Gobir ta nada Alan waka Danburan Sarkin Gobir

Likafa ta kara gaba, Alan waka ya zama Damburan Sarkin Gobir

Masarautar Gobir mai dumbin tarihi ta karrama fitaccen mawakin Hausa, Aminu Ladan Abubakar (Alan Waka) da sarauta a Masarautar ta Gobir.

Aminu Ala, ya wallafa takardar nadin da masarautar ta aike masa a matsayin Danburan Sarkin Gobir a shafinsa na Facebook ranar Talata 8, ga watan Disambar 2020.

Masarautar Gobir ta ce, ta nada shi ne bisa cancantarsa da kuma goyon bayansa gare ta da Gwamnatin Jihar Sakkwato.

Sarautar Danburan Sarkin Gobir a Masarautar Gobir, ta ’yan cikin gida ne da ake nada ’ya’yan Sarki.

Ba wa Alan wakar wannan sarautar ba zai rasa nasaba da dangantakar da mawakin ke da ita ba da Masarautar ta Gobir ta Bawa Jangwarzo.

Kafin nada shi Danburan Sarkin Gobir, Masarautar Bichi a Jihar Kano ta nada mawakin sarautar Dan Amanar Bichi; Masarautar Dutse-gadawur a Jihar Jigawa ta nada shi Sarkin Wakar kasar Dutse; sai kuma Masarautar Karaye a Jihar Kano da ta nada shi Dujuman Karaye.