Masarautar Gobir mai dumbin tarihi ta karrama fitaccen mawakin Hausa, Aminu Ladan Abubakar (Alan Waka) da sarauta a Masarautar ta Gobir.
Aminu Ala, ya wallafa takardar nadin da masarautar ta aike masa a matsayin Danburan Sarkin Gobir a shafinsa na Facebook ranar Talata 8, ga watan Disambar 2020.
- Asirin budurwa ya tonu bayan saurayi ya yi garkuwa da ita
- Dakarun Najeriya sun kashe ’yan Boko Haram a Borno
- Shugaban Media Trust ya zama sabon shugaban Kungiyar Masu Gidajen Jarida
Masarautar Gobir ta ce, ta nada shi ne bisa cancantarsa da kuma goyon bayansa gare ta da Gwamnatin Jihar Sakkwato.
Sarautar Danburan Sarkin Gobir a Masarautar Gobir, ta ’yan cikin gida ne da ake nada ’ya’yan Sarki.
Ba wa Alan wakar wannan sarautar ba zai rasa nasaba da dangantakar da mawakin ke da ita ba da Masarautar ta Gobir ta Bawa Jangwarzo.
Kafin nada shi Danburan Sarkin Gobir, Masarautar Bichi a Jihar Kano ta nada mawakin sarautar Dan Amanar Bichi; Masarautar Dutse-gadawur a Jihar Jigawa ta nada shi Sarkin Wakar kasar Dutse; sai kuma Masarautar Karaye a Jihar Kano da ta nada shi Dujuman Karaye.