Masarautar Bauchi ta tuɓe rawanin Sanata Shehu Umar Buba kan sukan Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed.
Sanata Shehu Umar Buba shi ne Majidadin Bauchi kafin a tsige shi bisa abin da masarautar ta kira rashin da’a da cin mutuncin Gwamna Bala Muhammed.
A baya-bayan nan ne Sanatan ya soki gwamnan bisa dora laifin matsin tattalin arzikin da ake ciki a Najeriya kan Shigan Kas Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnan ya zargi manufofin gwamnatin APC ta Tinubu da haddasa yunwa da kuncin rayuwa da suja haddasa zanga-zanga da ak gudanar a faɗin Najeriya.
Sanarwar da masarautar ta aike wa sanatan ta ce majalisarta karkashin jagorancin Sarkin Bauchi, ta yi zaman kan abin da ya kira rashin da’arsa.
Kuma a karshe ta yi ittifakin tube masa rawanin Majidadi.
Sanarwar ta ce ta samu Sanata Buba da laifin rashin ladabi da kuma wulakanta Gwamna Bala Mohammed, wanda hakan ya saba wa tarbiyyar Masarautar
Sanatan ya zargi gwamnan da zama ummul aba’isin talauci da yunwa da kuma fushin da al’ummar jihar ke ciki.
Ya kuma zargi gwamnan da rashin raba tireloli 70 na hatsi da wasu 70 na takin zamani da kuma 20 na shinkafa da gwamnatin Tarayya ta bayar domin raba wa al’ummar jihar.