Masarautar Bauchi karkashin jagorancin Sarki Rilwanu Suleiman Adamu, ta nada Muhammad Uba Ahmed Kari a matsayin sabon Wazirinta.
Sanarwar da Masarautar ta fitar ranar Alhamis mai dauke da sa hannun jami’in yada labaranta, Babangida Hassan Jahun, ta nuna za a yi bikin nadin sabon Wazirin ne ranar Juma’a.
- An binne Fafaroma Benedict XVI a Fadar Vatica
- An rufe gidajen mai 14 a Kano saboda sayarwa a farashin da ya wuce hankali
Ta ce, “Masarautar Bauchi na gayyatar ’yan uwa da abokan arziki zuwa wajen nadin sarautar sabon Wazirin Bauchi, Alhaji Muhammad Uba Kari, a ranar 6 ga watan Janairu, 2023 da misalin karfe 11:00 na safe a Fadar Masarautar Bauchi.”
Wannan na zuwa ne kimanin awa 48 bayan tube Alhaji Bello Kirfi daga matsayin Wazirinta da Masarautar ta yi.
Aminiya ta rawaito Masarautar ta tsige Bello Kirfi daga mukaminsa ne saboda zargin rashin biyayya ga Gwamnan Jihar, Bala Mohammed.
Sakamakon tube wa mahaifinta rawani a matsayin Wazirin Bauchi da Masarautar ta yi, ya sa Kwamishiniyar Bunkasa Kungiyoyi, Kanana da Matsakaitan Sana’o’i ta Jihar, Sa’adatu Bello Kirfi, ta yi murabus daga mukaminta.