✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jerin Manyan Dambarwan Kano a 2024

Jerin abubuwan da suka fara Kano da suka gwara kan jama'a a shekarar 2024

Shekarar 2024 na gab da ƙarewa, amma wasu abubuwa masu tayar da jijiyoyin wuya da suka faru a Kano ba za su gushe daga zukatan mutane cikin sauƙi ba. Rikicin masarautun Kano da da zangazangar yunwa da ta yi sanadin salwantar rayuka da dukiya, da dai sauransu, sun jawo ce-ce-ku-ce na tsawon lokaci.

Wannan rahoton ya zayyano muhimman abubuwa bakwai da suka ɗauki hankulan mutane a Kano cikin wannan shekara mai yin bankwana:

1. Saukar Shugaban Hisbah kan danbarwar ’yar Tiktok

A ranar Juma’a, 1 ga watan Maris, Sheikh Aminu Daurawa, Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ya yi murabus daga muƙaminsa bayan sukar salon aikinsa daga Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Sheikh Daurawa ya bayyana murabus ɗinsa ne a wani bidiyo da ya yaɗa a shafinsa na Facebook yayin gudanar da wani taro tare da ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano da aka yi a Kaduna. Inda ya bayyana cewa:

“Na ji wasu kalamai daga jihar Kano da suka ɓata min rai. Abin da nake ƙoƙarin yi a Hisbah shi ne gyara halaye da ɗabi’u. Amma na yanke shawarar yin murabus daga wannan matsayi.”

“Na yi duk mai yiwuwa wajen gayyatar masu shirya fina-finai, kuma mun tattauna sosai kan yadda za mu aiwatar da manufarmu.

“Amma ina neman afuwar gwamna. Ina so ya sani cewa na ajiye muƙamin da ya bani a Hisbah. Kuma ina roƙon Allah Ya ba shi nasara a gwamnatinsa,” in ji shi a cikin bidiyon.

A ranar Alhamis, 29 ga Fabrairu, Gwamna Yusuf ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda jami’an Hisbah suka gudanar da wasu samame a wuraren da suka yi ƙaurin suna a ƙarshen shekarar da ta gabata, yayin wata ganawa da limamai a Fadar Gwamnati.

Ya yi wa Hisbah gargaɗi kan yadda jami’ansu suka muzguna wa matasa maza da mata, sannan suka jefa su cikin motoci da ƙarfin tsiya yayin samamen.

Gwamnan ya bayar da misalin wasu bidiyoyi guda biyu da suka bazu a kafafen sada zumunta, inda aka nuna samamen Hisbah a wani wurin cin kifi kusa da Otal ɗin Sarina, da kuma wani samame a ɗakunan kwanan ɗalibai mata na Jami’ar Bayero da ke Kano.

Dalilin haka ne Gwamna Yusuf ya yi kira ga jami’an Hisbah da su sauya salon aikinsu, ta hanyar gudanar da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, sannan su miƙa waɗanda ake zargi ga hukumomin da suka dace.

Abin mamaki kan kalaman gwamnan shi ne a daidai lokacin da ake cikin cecekuce kan wata ‘yar TikTok mai suna Murja Kunya, wacce ta fito fili tana goyon bayan Gwamna Yusuf, kuma aka sake ta daga gidan yari cikin yanayi da ba a bayyana ba, alhali tana fuskantar shari’a a kotun shari’a bayan kama ta da jami’an Hisbah su kayi.

Bayan shiga tsakani da dattawa su kayi, Sheikh Daurawa ya koma bakin aikinsa a matsayin Shugaban Hisbah.”

2. Rushe masarautun Kano

Rushewar masarautun Kano ta hanyar dokar “Kano Emirates Council (Repeal) Bill 2024” wacce Gwamna Yusuf ya sanya wa hannu, ta jawo babban rikici a jihar. Wannan doka ta cire Sarki Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu da tsohon gwamna Ganduje ya naɗa.

Gwamnan ya ba dukkan sarakunan da abin ya shafa wa’adin awanni 48 su fice daga fadarsu kuma su miƙa ragamar mulki ga Kwamishinan Harkokin ƙananan Hukumomi da Sarautu. An mayar da Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarki, kuma ya jagoranci sallar Jumu’a a fadar gwamnati jim kaɗan bayan karɓar takardar naɗinsa a hukumance.

Aminu Ado Bayero ya koma birnin Kano da safiyar ɗaya daga cikin ranakun bayan an tuɓe shi daga mulki, inda ya tare a ƙaramar fadar Nasarawa, ina daga can zai ci gaba da gudanar da mulkinsa na sarauta.

Daga bisani, shari’a ta biyo baya, inda kotuna suka bayar da umarnin da ke karo da juna wajen tabbatar da matsayin sarautar sarakunan biyu.

Wata babbar kotun tarayya ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Muhammad Liman ta bayar da umarnin wucin gadi da ya hana amfani da sabuwar dokar, yayin da wata kotun jiha ƙarƙashin Mai Shari’a Amina Aliyu ta kuma hana Aminu Ado Bayero ya ci gaba da bayyana kansa a matsayin sarkin Kano.

Haka nan, kotun ta hana tsoffin sarakunan Bichi da Rano da Gaya da na Karaye su bayyana kansu a matsayin sarakuna.

Wata babbar kotun tarayya ƙarƙashin Mai Shari’a Simon Amobeda a watan Yuni ta tabbatar da tsige Aminu Ado Bayero daga mulki tare da bayar da diyya ta Naira miliyan goma ga sarkin saboda umarnin da aka bayar na kama shi da kuma korarsa daga fada.

Rikicin ya kai ga kafa kotuna dabandaban, tare da umarnin masu sassaɓawa juna kan wanda ya cancanci ya zama sarkin Kano. Yayin da shari’ar ke ci gaba a kotun ɗaukaka ƙara, sarakunan biyu suna samun kariya daga gwamnati.

3. Wani ya cinna wuta a masallaci ya ƙona masallata

A ranar 15 ga Mayu 2024, wani mutum mai suna Shafi’u Abubakar, mai shekara 38,

ya ƙona mutane 23 da suka taru don sallar asuba a wani masallaci a ƙauyen Albasawa da ke ƙaramar Hukumar Gezawa. Ana tuhumar Abubakar da laifuka da suka haɗa da kisan kai kuma idan aka same shi da laifi, zai fuskanci hukuncin kisa.

Wannan mummunan al’amari ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 23 da suka taru domin yin sallar asuba, inda aka ƙone su har lahira.

An gurfanar da wanda ake zargi a gaban Babbar Kotun Shari’a bisa tuhumar kisan kai da gangan, yunƙurin kisan kai da haddasa munanan raunuka da kuma haddasa ɓarna ta hanyar kunna wuta.

Lauyan masu gabatar da ƙara kuma Daraktan Gabatar da ƙara (DPP) a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, Salisu Tahir, ya shaida wa kotu cewa laifukan sun ci karo da sassa na 220 da 140 da 148 da 167 da kuma na 370 na Dokar Laifuka ta 2000 ta Jihar Kano.

Wanda ake zargi ya amsa dukkan tuhumar da ake masa, sannan masu gabatar da ƙara suka rufe shari’arsu a ranar 12 ga Nuwamba. Idan an same shi da laifi, dokar sashe na 220 na Dokar Laifuka ta tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ko harbi.

4. Zanga-zangar yunwa

Zanga-zangar yunwa da aka gudanar a ranar 1 ga watan Agusta ta rikiɗe zuwa tashin hankali inda mutane uku suka rasa rayukansu bayan lalata wasu shaguna da ɓarnata wasu gine-ginen gwamnati.

Gwamna Yusuf ya sanya dokar ta-ɓaci ta sa’o’i 24 a jihar, yayin da aka kama mutane 269 bisa zargin tada hankalin jama’a.

A ranar Juma’a, 2 ga watan Agusta, titunan Kano sun kasance babu kowa tare da dakatar da duk wani motsin ababen hawa. Rundunar haɗin gwiwa ta ‘yan sanda, jami’an tsaro na NSCDC, da ƙungiyoyin sa-kai na gari sun kafa shingaye a wurare masu muhimmanci, suna hana mutane zirga-zirga.

‘Yan sanda a jihar sun bayyana cewa sun kama mutane 269 a ranar Alhamis bisa zargin yin amfani da zanga-zangar yunwa ta ƙasa baki ɗaya don fasa shaguna da lalata dukiyar gwamnati.

A rana ta biyar ta zanga-zangar, wasu masu ɗauke da tutocin ƙasar Rasha sun bayyana inda suka gudanar da addu’o’i na musamman a jihar. An hangi masu riƙe da tutar suna gudanar da zanga-zangar a wurare kamar titin Kano-Zariya da titin gidan Zu, da titin Hadejiya da sauran wurare. Wasu daga cikinsu an kama su kuma aka wuce da su zuwa Abuja.

5. Dambarwar Kwangilar magunguna

Rikici ya barke kan wata yarjejeniyar magunguna ta Naira miliyan 440 da ta shafi kananan hukumomi 44 na jihar. Musa Garba, wanda ke da alaƙa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, an bincike shi da wasu jami’ai bisa zargin almundahana. Amma tun daga lokacin ba a sake jin labarin binciken ba.

PCACC ta ƙaddamar da bincike kan zargin damfara a kwangilar samar da magunguna a ƙananan hukumomi 44 na jihar, wanda aka ƙiyasta kuɗinsa ya kai Naira miliyan 440. Hukumar ta gano wata matsala a kwangilar gyaran rijiyoyin burtsatse, wanda aka ƙiyasta kuɗinsa ya kai kusan Naira miliyan 660.

Binciken ya kai ga tuhumar wasu jami’ai, ciki har da Sakatare Dindindin na Ma’aikatar Harkokin ƙananan Hukumomi da Masarautu, Mohammed Kabara da Shugaban reshen jihar na ƙungiyar ƙananan Hukumomin Nijeriya (ALGON), Abdullahi Ibrahim Bashir da wasu jami’ai na Ma’aikatar ƙananan Hukumomi, waɗanda aka fara tsarewa.

Daga bisani, mai kamfanin Noɓomed Pharmaceuticals, Musa Garba, ya bayyana a gaban masu bincike tare da lauya mai kare shi, Okechukwu Nwaeze. Tun daga lokacin ba a sake jin wani abu daga hukumar ba.

6. Hatsaniyar kwamishiniya da likita

ƙungiyar Likitoci ta Nijeriya (NMA) ta janye ayyuka daga Asibitin Murtala Muhammad bayan wani rikici tsakanin ƙwamishiniyar Jin ƙai da wata likita.

Ba wannan ne karo na farko da likita ke fuskantar cin zarafi daga dangin marasa lafiya ba, waɗanda galibi ke zargin ma’aikatan lafiya da rashin yin aiki cikin gaggawa.

Amma Kakakin ƙungiyar Likitoci ta Nijeriya (NMA), Dakta Muhammad Aminu Musa, ya ce binciken da Ma’aikatar Lafiya ta gudanar ya tabbatar da cewa likitar ba ta yi kuskure ba a lamarin, inda aka tabbatar da cewa ta yi aiki cikin cikakkiyar ƙwarewa.

“Duk da haka, ba a ɗauki wani mataki ba don magance rashin ɗa’ar Kwamishiniyar Harkokin Jin ƙai, wadda ta jagoranci wannan cin zarafin kuma ta tsangwami ma’aikaciyar lafiya da take gudanar da aikinta a ƙarƙashin mawuyacin hali.

Wannan ya jawo cece-kuce har sai Gwamna Yusuf ya shiga tsakani kuma aka warware matsalar.

7. Dakatar da Sakataren Gwamnati da kwamishina

Jam’iyyar NNPP ta Kano ta dakatar da Sakataren Gwamnati Abdullahi Baffa Bichi da Kwamishinan Sufuri Muhammad Diggol a ranar 14 ga Oktoba saboda zargin rashin ɗa’a da goyon bayan wata ƙungiya mai suna “Abba Tsaya da ƙafarka” wacce ake ganin tana neman ruguza tasirin Kwankwasiyya.

Har ila yau, wasu ‘yan majalisar NNPP biyu, Aliyu Madakin Gini da Kabiru Alhassan Rurum, an zarge su da ingiza rikicin, bayan da suka fito fili suka nuna goyon bayansu ga NNPP ƙarƙashin jagorancin Chief Boniface Aniebonam, wacce ta yanke alaƙa da tafiyar Kwankwasiyya