✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Akure ta ba da umarnin rufe shaguna saboda bikin al’ada

Umarnin na iya ranar Juma'a ne kawai, in ji masarautar

Masarautar Akure da ke Jihar Ondo ta umarci ’yan kasuwa su rufe shaguna da kasuwanni a ranar Juma’a saboda bikin al’ada na Aheregbe da aka saba yi duk shekara.

Deji na Akure Oba Adetoyinbo Ogunlade Adelusi ne ya bayar da umarnin rufe dukkan kasuwannin a cikin wata sanarwa da Sakataren Labarai na Fadar Sarkin, Michael Adeyeye ya raba wa ’yan jarida a Akure, babban birnin Jihar ranar Alhamis.

Sai dai sanarwar ta ce umarnin bai shafi kantunan sayar da magani da asibitoci ba, kuma bai hana zirga-zirgar jama’a da abubuwan hawa a fadin masarautar ba.

Oba Adetoyinbo Ogunlade Adelusi ya roki dukkan mata ’yan kasuwa da masu shagunan kasuwanci su yi aiki da wannan umarni bukukuwan al’ada na bana.

Aminiya ta tambayi Sarkin Hausawan Akure Alhaji Babangida Sa’idu Kusada cewa ko wannan umarni ya shafi mutanensa? Sai ya ce, “Kwarai da gaske wannan umarni ne da ya shafi dukkan kabilu ’yan gari da baki. Kuma tun shekarun baya ake yin irin wannan bikin al’ada a masarautar Akure.”

Sai dai ya ce umarnin zai yi aiki ne kawai a ranar Juma’a.

Sarkin Hausawan ya ce tuni suka umarci al’ummarsu a Jihar, da su girmama umarnin.

Yayin bikin dai, basaraken ma Akure ya kan shiga wata rijiya da zai kasance a cikinta har zuwa rana irin ta gobe da zai fito da iyalai da fadawansa za su taya shi murna da ci gaba da gudanar da bikin a al’adance.