Shugabar Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta ce kasar Masar za ta maido da ‘yan Najeriya bakwai cikin su takwas da suka yi zanga-zangar #EndSARS a kasar ta ba bisa ka’ida ba.
Dabiri-Erewa, a jerin sakonnin da ta wallafa a shifinta na Twitter ta ce ‘yan Najeriya da dama sun roke ta ta taimaka a sako su.
Ta ce, “Sabon labari kan ‘yan Najeriya 8 da ke tsare a Masar bisa laifin zanga-zangar ba tare da izini ba shine hukumomin Masar sun ce za su maido bakwai daga cikinsu.
“Ana zarginsu ne dai da gudanar da zanga-zanga a ranar 18 ga watan Oktoba ba tare da samun izinin zama kasar ko biza ba.
“Daya daga cikinsu, wanda ke da izinin zama, zai cika takardar rantsuwa a ofishin Ministan cikin gida na kasar, Mahmoud Tawfik, kan cewar ba zai kara aikata irin laifin ba, a tsawon lokacin da zai zauna a kasar,” inji Dabiri-Erewa.
Idan ba a manta ba, an kama ‘yan Najeriya ne a birnin Kairo na kasar ta Masar bisa laifin yin zanga-zangar zalunci da kisan gilla da ‘yan sanda ke yi wa mutane a Najeriya.