✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Masar ta gargadi kocinta game da wasan

A shirye-shiryen tunkarar kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a garin Kaduna a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin Afirka da zai gudana a…

A shirye-shiryen tunkarar kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a garin Kaduna a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin Afirka da zai gudana a yau a garin Kaduna tsakanin Najeriya da Masar, Hukuma shiryar kwallon kafa ta Masar (FA) ta yi gargadi ga kocinta Hector Cuper cewa idan ya kuskura Najeriya ta doke Masar a wasanni biyun da za a yi, ko shakka babu zai rasa mukaminsa na kocin kungiyar.
Hukumar kwallon kafa ta Masar ta ce ba za ta lamunci Najeriya ta doke Masar a wasanni biyun za za a yi ba.
Hukumar ta ce ganin yadda Masar ce take kan gaba a rukunin G, ba za ta lamunci Najeriya ta karbe ragamar ba, idan ta samu nasara a wasannin.  Don haka hukumar ta yi gargadi ga kocin da ya yi duk mai yiwuwa ya ga Najeriya ba ta samu nasara a kan Masar ba.
Wannan gargadi ta sa kocin ya gayyato zaratan ’yan kwallonsa da ke Turai da suka hada da Salah na AS Roma da ke Italiya da Ahmed Elneny na kulob din Arsenal da sauransu don ganin sun ba marada kunya.
Don haka akwai bukatar Najeriya ta yi taka-tsan-tsan ganin komai zai iya faruwa a wasan.