Kasar Masar ta gargadi Habasha kan bayyanar wasu tsagu a fuskar daya daga cikin matattarar ruwan da ke jikin babban madatsar ruwa rRenaissance da ke Habasha.
Masar ta ce abin tashin hankali ne ganin yadda Habasha ta gaza gudanar da binciken ka’ida na tababbatar da ingancin tsaron muhalli da kuma tasiri ga rayuwa da tattalin arziki na madatsar ruwan.
Gargadin na cikin wata takardar koke ne da kasar ta aikawa Sakataren Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a cewar Jaridar Arab News.
Takardar koken na cewa, Ministan Noman Rani da Albarakatun Ruwa, Mohammed Abdel-Aty, ya samu wani sako dangane da aniyar kasar Habasha na ta fara cike babban madatsan ruwan a wannan damunar.
Wannan aniya, a cewar ministan, ya zo ne a daidai lokacin da babu wata yarjejeniya tsakaninta da Masar da kuma Sudan kan matakan cike tsagewar madatsar ruwan.
Hakan ya ce saba yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasashen uku wacce aka sa hannu a shekarar 2015.
Sannan ya jaddada cewa Masar za ta dorawa Habasha alhakkin duk wata barna da hakan ka iya jawowa kasarsa a sakamakon saba yarjejeniyar da suka yi a tsakaninsu.
Babbar Madatsar ruwan ta Renaissance ta kasance wata abar takaddama ce a tsakanin kasashen Masar da Sudan da kuma Habasha, a inda kowannensu ke da ruwa da tsaki kan kogin Nilu wanda aka gina madatsar ruwa a kan sa.