A shekaranjiya Laraba kasar Masar ta bi sahun Najeriya a kasashen da suka fara kaiwa wasan zagaye na biyu a gasar cin Kofin Afirka da yanzu haka ke gudana a Masar din.
Masar ta kai wannan matsayi ne bayan ta lallasa Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo da ci 2-0.
Ahmed Elmohady ne ya fara ciwo wa Masar kwallo, yayin da shahararren dan kwallon Liberpool Mohammed Salah ya zura kwallo ta biyu.
Ita ma Masar kamar Najeriya ta samu nasara a wasanni biyun da ta yi ne wanda hakan ya sa ta kai zagaye na biyu duk da tana da sauran wasa daya.
Masar ce ta fi kowace kasa yawan daukar wannan kofi na Nahiyar Afirka inda kawo yanzu ta dauka sau 7 yayin da Najeriya ta dauka sau uku.
Yanzu dai ana jiran sakamakon fafatawar da ake yi ne a sauran rukunan don tantance kungiyoyi 14 da za su haye zagaye na biyu.