A kasar Masar, an dakatar da wani farfesa bisa zargin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W) yayin wata gardama tsakaninsa da dalibansa.
Farfesa Muhammad Mahdaly ya rasa aikinsa ne bayan da ya bayyana ra’ayinsa kan wani zanen batanci da mujallar Charlie Hebdo ta kasar Faransa ta wallafa yayin gardamar da daliban nasa.
- An fille kan malamin da ya yi batanci ga Annabi
- Batanci ga Annabi: Shugaban Turkiyya ya bukaci a daina sayen kayan Faransa
Mahdaly, wanda Farfesa ne a bangaren koyar da ilimin zamantakewar dan Adam dai tun da farko daliban sun zarge shi da furta kalamai marasa dadi a kan Musulunci yayin da yake koyarwa a aji.
Kazalika, a wani bidiyo da ya karade shafukan zumunta, an ga Farfesa Mahdaly na sukar ayoyin Kur’ani a yayin da yake wata tattaunawa kan batun aure da biyan sadaki da kuma saki a Musulunci.
Bugu da kari, a wani bidiyo na daban kuma, an gan shi yana caccakar yanayin zamantakewar Musulmai inda ya ce abin da suke yi ba shi da asali.
Kalaman nasa sun harzuka mutane da dama musamman a kafofin sada zumunta a kasar, inda suke ta Allah-wadai da shi.
Tuni dai Ministan Ilimin Gaba da Sakandare na kasar Masar ya bayar da umarnin dakatar da Mahdaly tare da kaddamar da bincike a kansa.
Zanen da mujallar Charlie Hebdo ta yi a kwana-kwanan nan da kuma yadda shugaban kasar, Emmanuel Macron ya nuna goyon bayansa kan hakan ya jawo zanga-zanga da la’anta daga kasashen Musulmai da dama ciki har da kasar ta Masar.