Ƙungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya (MAN) ta ce ’ya’yanta sun yi kwantai na kayan Naira biliyan N271.96 a watanni shida na farkon shekarar 2023 da muke ciki.
Rahoton tattalin arzikin Najeriya na rabin shekara da ƙungiyar ta fitar ya nuna kayan da masana’antu suka sarrafa da suka yi kwantai a watanni shidan sun haura kwantan biliyan 187 da suka yi a irin lokacin a 2022 da Naira biliyan 85.
- NAJERIYA A YAU: ‘Yadda yawan ciyo bashi zai durƙusar da Najeriya’
- DSS ta cafke Babban Editan jaridar Al-Mizan
Rahoton ya alaƙantan asarar da suka yi da matsin tattalin arziki, wanda ya kawo raunin aljihun masu sayen kayayyakin masana’antu a Najeriya.
Ƙungiyar ta bayyana cewa masu masana’antu sun tafka asarar ce duk da kuɗaɗen da suka kashe a tsawon lokacin sun ƙaru zuwa Naira biliyan 192.8 daga Naira biliyan 178.3.
Ta bayyana cewa ƙarin kashe ƙudin ya faru ne a sakamakon faɗuwar darajar Naira, daga N462 zuwa N901 a kan Dala ɗaya a tsawon lokacin.
“Ba za a ga inda aka kashe kuɗaɗen a zahiri ba, saboda ƙudin kayayyakin sarrafawa da na injunan da aka saba ne suka ƙaru,” kamar yadda rahoton ya bayyana.
An rage ma’aikata
Ƙungiyar ta bayyana cewa a sakamakon haka, masana’antu sun sallami kashi 32 na ma’aikatansu, lamarin da ya sa ma’aikatansu raguwa daga 9,559 a 2022 zuwa 6,428 a watanni shidan farko na 2023.
Haka kuma masana’antu 313 sun daina aiki a tsawon lokacin, daga cikin 6741 da ake da su a 2022.
Rahoton ya ce yawan masana’antu da ke daina aiki da kuma sallamar ma’aikata sun faru ne “a sakamakon tsare-tsaren da gwamnati ta yi hanzarin aiwatarwa a ɓangaren daga 2022, musamman canjin kuɗi da dokar takaita cirar tsabarsu.
Ma’aikata 3,567 ne suka rasa ayyukansu a watanni shidan farko na 2013, sabanin 1,709 a kwatankwacin lokacin a 2022.