✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masallacin da ake aikin gina shi a Nguru ya rushe, ya kashe mutum 4

Ginin ya riga ne lokacin da ake mika kankare a saman masallacin

Wani masallaci da ake kan gina shi a garin Nguru na Jihar Yobe ya rushe tare da halaka leburori hudu da jikkata wasu mutum 13.

Masallacin da ya rushe dai yana kan hanyar Machina ne da ke da nisan kilomita uku daga cikin garin na Nguru.

Rahotonni na nuni da cewar masallacin, mai suna Madinatul Ngibirwa, wani malamin addinin musulunci Sheik Khalifa Fatiu ne ke kula da shi.

Wani malami da ke kusa da masallacin yayin da wannan iftila’in ya faru da bai amince a fadi sunansa ba ya shaida wa Aminiya cewar, yadda ake ginin masallacin nan babu wata alamar cewar zai iya rushewa.

Shi kuwa Malam Nasiru, wani mai sayar da bakin mai garin na Nguru ya, tabbatarwa da wakilin Aminiya cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis ne wajen karfe 5:00pm na yamma.

Ya ce ginin ya rushe ne lokacin da ake tsaka da gudanar da aikin mika kankare don zubawa a saman masallacin, sai ya kasance mutanen sun yi wa ginin yawa.

Malam Nasiru ya ce hakan ce ta sa nan take ginin ya rufta kasa, wadda hakan ne ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane hudu tare da jikkata mutane da dama.

Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin injiniyan da ke kula da aikin ginin ya ci tura kasancewar baya nan.