✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maryam Jummai Bello: Ba kudi ne komai a rayuwa ba

Maryam Jummai Bello Jami’ar Bincike ce a Hukumar Petroleum Ekualization Fund, kuma mamba ce a taron kasa da aka kammala. Ita ce kodinetar kasashen Yammacin…

Maryam Jummai Bello Jami’ar Bincike ce a Hukumar Petroleum Ekualization Fund, kuma mamba ce a taron kasa da aka kammala. Ita ce kodinetar kasashen Yammacin Afirka a karkashin hukumar zirga-zirga ta duniya da ke da hedikwata a Landan. Ta yi bayanin yadda ta yi gwagwarmayar rayuwa da irin gudunmuwar da suka bayar yayin taron kasa. Ta bukaci matan auren su rika lura da mijinsu.

Tarihin Rayuwata
Assalamu alaikum, sunana Maryam Jummai Bello. Ina aiki da Hukumar Petroleum Ekualization Fund. Ni mamba ce a taron kasa da aka kammala a Abuja. Yayin taron ina cikin kwamitin da suka shafi harkokin mai da iskar gas, mun kuma bayar da bayanan yadda harkar man fetur da iskar gas za ta inganta a kasar nan.
Ni matar shugaban kungiyar NURTW na kasa ne, kuma ni ce shugabar kungiyar matan shugabannin kungiyar NURTW ta kasa. Yanzu kuma ni ce kodinetar kasashen Yammacin Afirka ce a karkashin kungiyar zirga-zirga ta duniya da ke da hedikwata a birnin Landan (International Transport Federation). An yi zaben ne a kasar Habasha, kuma ni ne zan rika duba ayyukan kungiyar a kasashen Yammacin Afirka.
Asalina ’yar kauyen Utai da ke karamar Hukumar Wudi a Jihar Kano ce. Ni Bafulatana ce. Muna da yawa a wurin mahaifanmu. Mahaifina Yarima ne. Na yi makarantar firamare da ake kira Fagge Senior Primary School a Kano, sannan na kammala sakandaren Teachers College da ke Kano a shekarar 1976, inda a shekarar 1981 na yi N.C.E a bangaren Turanci da kuma Addinin Musulunci.  A shekarar 1991 na kammala digirina a bangaren Tsare-tsaren Koyar da Turanci a Jami’ar Jos. Na kammala digirina da digiri-mai-daraja-ta-biyu. Daga baya na yi digiri na biyu a bangaren Gudanarwa da tsare-tsare a bangaren Turanci, yanzu kuma ina digiri na uku don zama Dokta.
Abubuwan da ba zan manta da su ina karama ba
Akwai wani abu da ya faru da ni da ba zan taba mantawa da shi a rayuwata ba, wannan abun ya zama mini babban darasi a rayuwata, domin ya koya mini ladabi, biyayya da kuma da’a; ya koya mini tarbiyya, sannan ya sanya na kasance mai kwazo da jajircewa a kan duk wani abu da na sanya a rayuwata.
Mahaifina ba ya daukar wargi, hakan ya sanya mu ’ya’yansa muke gani ya cika zafi; muke ganin kamar yana takura mana. Baya wasa da bibiyar duk wani abu da ’ya’yansa suke yi ba. Misali idan dansa ya zo na daya a ajinsu, zai ba shi da kyauta mai gwabi. Idan kuma ba ka yi kokari ba, to ba zai saya maka ko da takalmi ba ne, haka za ka rika zuwa makaranta babu takalmi a kafarka. A lokacin sai mu samu fanko, mu bula shi a wurare uku, kamar yadda na takalmi silifas yake, haka za mu rika yi har zuwa lokacin da za mu yi kokari a makaranta. Idan kuwa muka yi kokari har kasuwar Bata za a je a sayo mana takalmi mai kyawu da kuma tsada, hakan ya ba mu damar jin kai da takama idan mun sanya takalmi mai tsada zuwa makaranta.
Abin da yake ci mana rai shi ne, idan ba ka yi kokari ba, haka za ka rika ganin ’yan uwanka suna tafiyar takama bayan sun sanya takalma masu kyawu da kuma tsada, kai kuma kana tafiya da silifas din fanko. A lokacin ba mu gane darasin da yake so ya koya mana ba, musamman ma yadda yake so mu mayar da hankali wajen karatu.  
Mahaifinmu ba ya wasa, idan mun dawo daga makaranta haka zai rika duba jakankunanmu kafin mu shiga cikin gida, don haka ba za ka shiga gidansa da kayan wani ba, wannan ya hana mu kwadayin daukar kayan wani; ya hana mu karbar aron kayan wasu mu shigo da su gida, hakan ya taimaka mana musamman ma ni, yanzu da nake sashin bincike a ofishinmu, mutane da yawa ba sa son mu’amala da ni, saboda na fi so a yi komai cikin gaskiya. A yanzu jama’a sun dauka kudi shi ne komai, sun manta shaida mai kyawu ita ce, komai ba wai yawan biliyoyin kudin da ba a same shi ta hanya mai kyawu ba.
Shakuwa tsakanini iyaye
Na fi shakuwa da mahaifina, ina kama da shi sosai, na koyi abubuwa da dama a wurinsa. Mahaifina maraya ne, domin jim kadan bayan mahaifiyarsa ta haife shi ta rasu, ba ta shayar da shi ba, don haka wadanda suka santa bayan an haife ni sai suka ce masa ina kama da ita, kamar an tsaga kara. Ina kaunar mahaifina sosai, har ta kai idan ba shi da lafiya sai in rika jin rashin lafiyar a jikina ko da ina nake kuwa. Duk wurin da nake sai na zo na gan shi kafin hankalina ya kwanta, lokacin da ya rasu na halarci wani kwas a Landan, kwana biyu kafin in je Landan na same shi muka yi sallama, bayan ya rasu ba a fada mini, hakan ya sanya da na tashi dawowa na sayo masa agogo kasancewar yana son agogo sosai, na kuma sayo masa takalma, domin ina tunanin zan same shi a gida.  A lokacin sun boye mini domin sun ce jikinsa ne kawai ya tashi, hankalina bai tashi sosai ba, domin na yi tsammanin irin rashin lafiyar da ya saba ne musamman ma da yake ya tsufa. Sun boye mini saboda shakuwar da muka yi. Bayan na dawo gida na samu labarin ya mutu sai hankalina ya tashi, na yi masa addu’a.
Burina ina karama
Na fara makarantar ’yan mishan da ake kira St. Thomas Primary School kafin na koma Fagge Senior Primary, a lokacin ina magana da Turanci sosai, hakan ya sanya hankalin ’yan gidanmu ya tashi, domin an fara rade-radin za a rinjaye ni in koma Kirasta, ko kuma za a wayi gari wata rana su gudu da ni, inji su wai yadda suke kauna ta, to komai zai iya faruwa. A lokacin kawayena suna kira ‘Maryam Ingilishi’ idan suna so in yi magana da Turanci sai su sanya ni a tsakiyarsu, sannan su ba ni biskit.

An yi mini aure kafin in kammala sakandare, musamman da iyayena suka tsorata kan rade-radin da ake ta yi a kaina. Alhamdulillah bayan na yi aure sai mijina ya fahimci muhimmancin ilimi, kuma ya bar ni na ci gaba da karatu.
Yadda na hadu da mijina  
Wata rana ni da kawata mun tsaya a wani wurin da ake sayar da kifi don mu saya, muna ciniki ke nan sai ya zo wurin, dama kuma kawata ta san shi, sai suka gaisa, a nan ya fada mata cewa ina burge shi, in da ta fada masa cewa zai yi wuya in amince da shi, muka yi dariya gaba daya, kafin ka ce wani abu sai muka fara soyayya, har muka yi aure.
Yana matukar sona, miji ne nagari.  Kai da ana mutuwa a sake dawowa, to zan ce ko na sake dawowa ina so ya sake zama mijina.
Shawara ga mata
Abin da yake burge mijina game da ni, shi ne, tun da muka yi aure ni nake yi masa girki, na kuma yi sauran aikace-aikacen gida, abin da yake ba shi mamaki shi ne, yawancin matan da suka kai wani matsayi a rayuwa sai su rika ganin sun fi karfin su rika aikin gida, don haka dole a dauko musu masu aikin gida. Don haka ya kamata mata su sani babban abin da ya kamata mu sanya a gaba shi ne, lura da maigidanmu da kuma gida, duk wani abu bayan su ba su zama mana dole ba. Mu gane hakan shi ne zaman aure.
Sutura
Nakan sanya duk wani tufafi da zai tsare mini mutuncina, ina sanya tufafin daidai da yadda ofishina ya tsara, sannan ina sanya tufafi daidai da yadda duk wani taro da zan je ya tsara.
Kwalliya
Ban cika amfani da kayan kwalliyar da za su rika mayar da ni mai karancin shekaru ba, ba na yin kwalliyar da za ta zubar mini da mutunci. Babbar kwaliyata ita ce dariya da murmushi da kuma kyakkyawar mu’amala.
Abin da nake so a tuna ni da shi
Ina so a tuna ni a matsayin wacce ta taba rayuwar mutane ta hanya mai kyawu, hakan ya sa nake so in kafa kungiya mai zaman kanta ko kuma wata cibiya da za ta rika gyaran zuciya da halayen mutane, musamman masu shaye-shayen miyagun kwayoyi, sannan ina so in rika taimakon masu karamin karfi don rayuwarsu ta inganta. Addu’ata ita ce, Allah Ya cika mini burina.