✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Marubuta a Najeriya, Masu Karatu a Nijar: Nazari a kan bukatuwar jaridun Hausa a Kudancin Nijar (3)

Shawarwari kan abubuwan da za su kawo karbuwar jaridun Hausa aNijar:Jaridu da mujallu suna da matukar muhimmiyar rawa da suke takawa wajen kawo ci gaban…

Shawarwari kan abubuwan da za su kawo karbuwar jaridun Hausa aNijar:
Jaridu da mujallu suna da matukar muhimmiyar rawa da suke takawa wajen kawo ci gaban tattalin arziki da kuma kawo zaman lafiya ga kasa. Domin ta hanyar jaridu da mujallu za a iya wayar da kai da fadakar da jama’a da kuma cusa ra’ayi kamar yadda muka fadi maganar yada manufa (akida) a baya, duk wadannan za su samu a cikin kasar Nijar da ma makwabtanta. Wadannan abubuwa sun hada da ire-iren abubuwan da hukumomi da kuma gwamnati suke gudanarwa na kyautata rayuwar jama’arta, wanda hakan zai dada taimaka wa jama’a su san gwamnati tana gudanar da ayyukanta domin kyautata rayuwarsu. Sannan wata kafa ce ta bunkasa harkokin kauwanci, ta hanyar tallata wa ’yan kasuwa kayayyakin da suke sayarwa a cikin gida da kuma kasashen makwabtansu. In kuwa haka ne ya zama wajibi a ce an yi duk yadda za a yi wajen ganin an tanadi wasu abubuwa wadanda in an yi dacen samar da su, zai sa jaridar da za a kafa ta dore dindindin. Wadannan abubuwa su ne kamar haka:
1-Zuba jari na buga jarida da zai iya kaiwa shekara biyar ba tare da an waiwayi kudin ba. 2-Sanya akida ko manufa a duk lokacin da za a kafa wata jarida ta Hausa. 3-Rubuta labarai da jama’a suka fi son karantawa. 4-Samar da dabarun kasuwancin jarida a kowane yanki na kasar Nijar. 5-Hadin gwiwar masu son yin jarida a kasar Nijar don su samar da kwakkwarar jarida a kasar. 6-A sami tsawon lokuta ana yin tallar jaridun da labaransu a gidajen rediyo. 7-’Yan bokon Nijar Hausawa da masu son harshen Hausa su dinga bai wa jaridun Hausa goyon baya. 8-Hada hannu da wasu ’yan jarida na kasashen makwabtan Nijar don su samar wa jaridunsu na Hausa abokan hulda.
Idan har za a samu a aiwatar da wadannan dabaru, to tabbas bayan wani lokaci za a samu goyon bayan kamfanoni da hukumomi, wajen bai wa jaridun Hausa tallace-tallace (musamman wadanda suka shafi wayar da kan al’umar kasa) kamar yadda ake bai wa jaridun Faransanci.
Kammalawa:
Idan har za a rika shigar da jaridu da mujallun Hausa daga Najeriya duk da kasancewar za a iya samun wadannan jaridu da mujallu ta hanyar internet, duk da cewa wasu tsarin rubutun Hausa a Najeriya da Nijar ya dan bambanta, sannan babu wata manhaja ta koyar da Hausa daga hukumar Nijar a manyan makarantu kamar sakandare ko jami’a, (sai dai firamare), wannan ya nuna muhimmancin sako cikin Hausa a wajen mutanen Nijar kuma ya nuna cewa akwai masu karantawa a Nijar, sai dai marubutan ko mawallafan ne babu ko kuma ba su da dauriya.
A bisa wannan matsayi ne wannan takarda take nuna cewar matsalolin da ake dora wa gwamnati na rashin baiwa harshen Hausa da sauran harsunan gida muhimmanci ko rashin kwarewa a fannin rubutun Hausa  a matsayin hujjar rashin samun dorewar jaridu a Nijar, wannan hujjoji ba su yi kama da a ce sun hana masu kishin harshen Hausa dagewa a kan burinsu na kafuwar jaridar Hausa a Nijar ba, domin tsarin shigar jaridu da mujallu da Littattafan Hausa daga Najeriya zuwa Nijar ya nuna tsarin kasuwanci ne ya yi karanci daga wajen masu ruwa da tsaki a fannin Adabin rubutu a kasar Nijar, fakat. Amma akwai masu karantawa a Nijar, akwai kuma bukatuwar karatun, sai dai marubutan ko mawallafan da masu samar da kasuwar ne babu.
Bukatuwar samar da hanyar kyautata tsaro da bunkasar kasuwanci da bunkasa al’adu da zaman lafiya da mutunta juna musamman a halin da kasashen Nijar da Najeriya da Kamaru da Cadi suka samu kansu a yau, ya dada fito da muhimmancin samar da jaridun Hausa ga mutanen yankin da Hausawa da masu son karatun Hausa suke, kuma wadannan yankuna sun fi amfani da Hausar fiye da harshen hukuma wato Faransanci, sannan shi ne za a samu a wayar da kansu cikin inganci kuma a saukake. Don haka samar da dorarriyar jaridar Hausa a yankin Zinder da Maradi da Tahoua da kuma rabi na yankin Dosso musamman Dogon Dutsi da Gaya da yankin Agadez abu ne da gwamnati da kungiyoyin sa kai da ’yan kasuwa masu zaman kansu za su sake wa kallo.
Mun Kammala