✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Martinez zai zama kocin Portugal, Chelsea ta shiga zawarcin Thuram, Dzeko zai tafi United 

Atletico Madrid na son sake saye tsohon dan wasanta Alejandro Garnacho.

Chelsea ta fara tattaunawa da Borussia Monchenglabad don ganin yiwuwar sayen dan wasan gabanta, Marcus Thuram, a watan Janairun da ake ciki, in ji Fabrizio Romano.

Atletico Madrid na bukatar Manchester United ta biya fam miliyan 9.5, idan har tana son daukar Joao Felix matsayin aro, ko kuma ta biya fam miliyan 70 ta saye shi gaba daya, in ji Sunday Mirror.

Tsohon kocin Everton da Belgium Roberto Martinez ya cimma yarjejeniyar fatar baki da Portugal don horar da tawagar.(Athletic).

Roberto Martinez

Sai jaridar L’Equipe, wadda ta ce Zinedine Zidane ya ki amsa tayin horar da tawagar kwallon kafar Amurka.

Tottenham na harin golan Everton da Ingila Jordan Pickford, don ya maye gurbin kyaftin dinta Hugo Lloris, in ji Sunday Mirror.

Al Nassr ta saki dan wasan gaban Kamaru Vincent Aboubakar, wanda Manchester United ke nema, kuma ta yi hakan ne don samar wa Cristiano Ronaldo gurbi a kungiyar.(Al-Riyadh).

Manchester United da Newcastle da Arsenal har ma da Chelsea, sun nuna sha’awar sayen dan wasan Netherlands, Memphis Depay, wanda ake sa ran zai bar Barcelona cikin wannan Janairun nan.(Sport).

Crystal Palace ta shirya gogayya da Everton wurin sayen dan wasan Aston Villa, Danny Ings. (Sun)

Ana rade radin cewa dan wasan gaban Brighton Leondro Trossard zai iya komawa Chelsea ko Newcastle.(The Athletic).

Newcastle kuwa Moussa Diaby ta ke son daukowa daga Bayern Leverkusen idan kaka ta kare.(Bild)

Sai kuma Aston Villa wadda dab take da sayen mai tsaron bayan Sfaniya da Real Betis, wato Alex Moreno, a cewar Bild.

A Janairun nan ne, Shugaban Brighton Albion din Paul Barber, ya gargadi Liverpool da Chelsea cewa, duk mai son daukar Moises Caicedo daga cikinsu ya shirya biyan makudan kudi.(Metro).

A nan kuma Sky Sports ce ta ruwaio cewa Leeds na neman dan wasan gaban Hoffenheim, Georginio Rutter mai shekaru 20.

Haka kuma, Arsenal ta nuna sha’awar sayen matashin dan wasan Barcelona Alejandro Balde, in ji Sport.

Southampton kuwa na duba yiwuwar dauko dan wasan gaban Japan, Daizen Maeda da ke wasa a Celtic.(Sky Sports)

Shi kuwa daraktan wasanni a Roma Tiago Pinto, na da kwarin gwuiwa cewa mai tsaron bayan Ingila Chris Smalling zai tsawaita zamansa da kungiyar.(Football).

A Sfaniya kuwa, Atletico Madrid na son sake saye tsohon dan wasanta Alejandro Garnacho, da yanzu ke wasa a Manchester United.

To amma rahotanni sun ce da wahala United ta yadda matashin ya bar Old Trafford.(Fichajes)

Akwai kuma rahotannin da ke cewa Man United din na duba yiwuwar sayen Edin Dzeko na Inter Milan, wanda ya samu nasara zamansa a Manchester City.(Mail)

Sai kuma Tottenham da ke sa ido ga golan Brentford David Raya mai shekaru 27, don ya maya gurbin Hugo Lloris na tsawon lokaci.( Telegraph)