Rundunar ‘yan sanda a Jihar Imo ta ce hadimin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak ya fice daga dakin otel din da ya sauka ba tare da sanar da rundunar ba.
Kakakin rundunar, SP Bala Elkana ne ya bayyana hakan a wata sanarwa aka raba wa manema labarai a Owerri babban birnin jihar, ranar Lahadi.
Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindiga sun harbe Barista Ahmed Gulak ne a ranar Asabar da dare yayin da yake hanyarsa ta komawa Abuja daga Jihar Imo.
A cewar Kakakin, lamarin ya faru ne bayan da ‘yan bindiga da misalin karfe 07:20 na safiyar Lahadi, suka kai hari kan wata motar tasi kirar Toyota Camry dauke da Ahmed Gulak tare da wadansu mutum biyu da ke kan hanyarsu ta zuwa tashar jiragen sama.
Ya ce marigayin ya fita daga otel din Protea ba tare da ya sanar da ‘yan sanda ko kuma sauran hukumomin tsaro a jihar ba duba da yadda ake fama da matsalar tsaro a yankin Kudu maso Gabas musamman ma jihar Imo.
“Ya fice ba tare da samun rakiyar jami’in tsaro ko guda ba, sannan direban tasin da ya shiga ya bi hanyar da ba a saba bin ta ba domin zuwa tashar jiragen.
“’Yan bindigar guda shida da ke cikin wata mota kirar Toyota Sienna ne suka cimmai sannan suka harbe shi a yankin Umueze Obiangwu na Karamar Hukumar Ngor-Okpala da ke daura da tashar jiragen sama,” inji Kakakin.
A karshe ya ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Abutu Yaro, ya ba da umarnin bincike game da kisan gillar tare da girke jami’an ’yan sandan musamman a wurin da lamarin ya faru.