Yau ma kamar yadda muka saba, na ba masu karatun wannan shafi ne dama su tofa albarkacin bakinsu kan batutuwan da muke tattaunawa yau da kullum. Da fatar za a sha karatu lafiya.
AHMED ISA: Ka ji maganar gaskiya, da ma Allah Ya ce kowace al’umma zai ba ta shugaba daidai da halinta. Allah Ya sa mu daina wadannan munanan dabi’u da suka zama ruwan-dare ga al’ummar kasarmu.
MURTALA SIRAJO: Wannan magana gaskiya ce ya Shehin Malami, sai dai da yake su Hausawa suna cewa shi laifi tudu ne, take naka ka hango na wani, wannan shi ne matsalarmu, kullum muna jira shugabanninmu su gyara mana a lokacin da mu kuma mun kasa barin barnar balle ma a samu damar gyaran. Allah Ya kara lafiya da tsawon kwana ya Shehin Malami.
DAYYIB MUSTAPHA: Lallai kuwa Farfesa, da ma Bahaushe ya ce: Dan tari shi ya san yawan kifinsa, amma kowa ya gyara ya sani, kowa ya bata ya sani, Allah a kawo mana mafita a wannan kasa.
ABUBAKAR UBA: “…Kuma yau kwana goma sha tara, ka iske mutum goma sha tara duk sun zaka sun taru sun nade masa hannu shi dai.
Kuma yau kwana goma sha takwas, ka iske mutum goma sha takwas duk sun zaka sun taru sun nade masa hannu shi dai.
Ba kau fashin fadan yakai ba, wandara sai randa ya ji mai sama Ya aiko mar ran nan yana da abokin fama,” inji Dan Anache.
ASHIRU HAMZA: Haka suka dauka a ransu, cewa sai mun gyara sannan su gyara, wanda hakan ya sa suka kasa gano bakin zaren, sai su ga kamar tufkar suke ana warwara! Sun manta cewa aikinsu ne da hakkinsu su gyara batacce! Domin ko a cikin baki akwai baki-baki.
UMAR DANBALLAJE: Allah Ya gafarta Malam ni na zata Shugaba Buhari yana sane da duk halayyar nan ta ’yan Najeriya a lokacin da yake ta kokarin yin takara da cin zabe har karo uku sai a na hudu ya kai labari. Kuma na yi tunanin ya shirya tsaf domin tunkara da magance su. Babu ko shakka akwai irina miliyoyi masu irin wannan ra’ayi, wanda hakan ne ya sa suka amince da kuma ba shi kuri’u domin kawo karshen duk irin wadannan matsaloli, gami da tabbaci da bugun gaba da shi Buharin ya rika yi na cewa za a kawo karshen duk wadannan matsaloli tare da yin Allah wadai da rashin katabus da gwamnatocin da suka gabace shi suka yi a kan lamurran gyara.
AHMED IDRIS: Tabbas wannan mukala taka ta yi, Allah Ya sa ta kai inda ya dace. Kafin can mu ma ’yan kasa idan muna son gyaranta lallai mu fara gyarawa da kanmu kafin mu jira wani ya taimaka mana.
ASMA’U LAMIDO: Tunda aka fara cece-ku-cen gazawar Mai girma Shugaban Kasa, ban taba ganin rubutun da ya gamsar da ni irin wannan ba. Saboda haka ina kira ga mu talakawa masu dogon muryar kiran Shugaba ya gyara, ko in ce masu yekuwar suna kishin kasa da rayukan bayin Allah da ake kashewa da su fara bin wadannan matakan da Malam ya zayyano su ga ni.
SALISU SA’AD DOKA: Gaskiya ni fa ina ganin har yanzu gwamnati ya kamata ta kara zage dantse wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Saboda lokacin da aka zabi shugabannin nan sun san da ire- iren wadannan matsaloli na gurbacewar tarbiyyar al’umma kuma duk da hakan suka ce a zabe su za su kawo canji. Don haka ni dai a ganina duk da haka rashin kyakkyawan shugabanci shi ke taka muhimmiyar rawa a matsalolin nan. Lokacin magabata da aka samu shugabanci nagari ai abubuwa ba su kacame haka ba. Allah Ya kyautata aikin Malam!
RABI’U MUSA: Wallahi Farfesa ka ba da cikakken bayani a kan halin da muke ciki. Ya Allah! Kada Ka azabtar da mu saboda mabarnata da wawayen cikinmu. Ka kare mu daga sharrin wannan zamani, amin.
LORD HYDAR: Masha Allah! Allah Ya yarda da aikin Malam! Wato ke nan Malam kamata ya yi a ce kasa ta gyaru idan ana son sama ta yi kyau. Wannan ta hanyar duba da Buhari a matsayin Shugaba. To amma ina labarin alkawari ko kuma rantsuwar bauta wa kasa da mutanen da Shugaban ya dauka? Allah dai Ya sa mu dace!
ABUBAKAR MARAFA: Iyakar gaskiya ke nan. Kuma daga kin gaskiya sai bata. Idan za mu gyara kanmu mu gyara. Mutum daya ba ya iya gyara mutum miliyan dari biyu, wadanda kowa daga gindinsa akwai guntun kashi. Amma sai a fito a yi ta hargowa cewa kasa babu tsaro. Alhali ko gidajenmu mun kasa tsarewa. Mu dai yi karatun ta-natsu, mu fuskanci gaskiya mu daina yaudarar kanmu.
AMINU MUSA: Da girman kujerarka! Allah Ya taya ma. Haka batunka yake zahiri ba mu ji, kunnuwanmu sun bushe Kuma da yawa daga cikin ’yan Najeriya batattu ne. Babu Allah a ransu kowa na hankoron dirar wa tsara ta kowace hanya, Amma komai tsanani da masu jin dadi, bai kamata laifin wadansu ya shafi wadansu ba, mu yi addu’a watakila a zo daidai wajen da ’yan amin din za su amsa sai kwatsam a wayi gari lamarin ya zama tsohon zance.
MAHADI DANBINTA GUGA: Wannan sharhi da galmi yake; har ya tuna min da “Kukan Kurciya Jawabi ne” a “Magana Jari Ce”! Allah ga bayinKa, Baba ya gaza aikinsa ya koma tunanin masu laifi ne za su yi masa aikinsa. Yana suka, ’yan kasa na suka. Ana kashe mu ana karyatawa, muna kwana da yunwa ana kiranmu ragage, ana ta bajet duk shekara a kan bashi kuma ana cewa ana tara makudan kudin shiga kuma ana kwato na barayi! Farfesa Malumfashi Ibrahim Allah Ya kara basira. Sannu da kokari. Ka fadi abin da suke so a fadi, abin da kawai ka manta shi ne ka ce; “Ya Shugabana Mai girma Baba Buhari ka sha kuruminka don hisabin ma a Lahira ’yan kasa za a yi ma wa domin su ne suka ki sauke nauyin da ke kanka!”
KABIR SAKAINA: Ya Allah! Ka bude mana kunnuwanmu don jin gaskiya, Ka kuma bude mana zukatanmu don gaskiya ta samu gurbin zama. Farfesa, Allah Ya saka maka da mafificin alheri.
RAHMA ABDULMAJID: Allah Ya sa kada su auno maka bakar magana. Akramakallahu
DARDA’U SAFANA IDRIS: Allah Ya saka da alheri Malam, Allah Ya kara maka lafiya da tsawon kwana.
ABDULKADIR BADAMASI: Wannan shi ne tsirarar gaskiya, Allah Ya taimaki Malam. Al’amarin kasar nan yana matukar ba ni tsoro, wallahi Buhari wahalar da kansa kawai yake yi.
NURA USMAN JANI: Allahu Akbar! ka ji bayani na gaskiya daga bakin mutane masu daraja, Allah Ya kara lafiya Malam, insha Allahu sai na yi digiri a Hausa komai daren dadewa!!!